Gwamnatin mulkin soji ta Jamhuriyar Nijar, karkashin jagorancin Janar Abdourahamane Tchiani a ranar Lahadin da ta gabata ne ta sanar da kwance duk wata yarjejeniyar soji da ta kulla da Amurka.
Hakan na kunshe ne acikin wata sanarwa da aka fitar daga gwamnatin jamhuriyar Nijar.
- Ramadan: Sanata Yari Ya Buƙaci Musulmi Da Su Yi Wa Shugaba Tinubu Addu’a
- Lauyoyi Mata Sun Koka Kan Cin Zarafin Da Alkalai Maza Ke Yi Musu A Adamawa
In ba a manta ba, ‘yan watannin da suka gabata, hukumomin sojin sun kwance irin wannan alaka da sojin Faransa daga bisani kuma aka nemi sojin Faransa da su fita daga Jamhuriyar ta Nijar.
Kasar Nijar dai, a shekarar 2013 ne ta kulla yarjejeniyar soji da kasar Amurka da Faransa wadda a karkashinta dakarun Amurka da ke Sahel suke amfani da kananan jiragen sama marasa matuka wajen yakar kungiyoyi masu ikirarin jihadi a yankin.
Tun bayan juyin Mulki, hukumomin soji a Jamhuriyar Nijar suka janye jakadunsu daga kasashen Amurka, Faransa, Nijeriya da kuma Togo