A yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aika da sako ga takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, don taya shi murnar sake lashe zaben shugabancin kasar.
Shugaba Xi ya ce, a shekarun nan, jama’ar kasar Rasha suna ta kokarin tinkarar kalubaloli bisa hadin gwiwarsu, inda suke ta samun nasarori a fannin raya kasa. A cewarsa, yadda shugaba Putin ya sake cin zabe a wannan karo ya shaida goyon bayan da al’ummar kasar Rasha suka nuna masa.
Shugaban na kasar Sin ya kara da cewa, Sin tana dora matukar muhimmanci kan huldar dake tsakaninta da kasar Rasha, kana kasar na son ci gaba da kokarin mu’ammala tare da bangaren Rasha, don tabbatar da ganin ci gaban huldar hadin gwiwa tsakanin kasashen 2, wadda ta shafi manyan tsare-tsare, da ayyuka na dukkan bangarori, gami da ganin yadda huldar za ta amfani al’ummun kasashen 2. (Bello Wang)