A yau Litinin, ma’aikatar harkokin wajen Sin ta gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda a gun taron wani dan jarida ya yi tambayar da ta shafi taron kolin dimokuradiyya da Koriya ta Kudu ke karbar bakunci yanzu haka.
Game da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian, ya bayyana cewa, a ko da yaushe bangaren Sin yana adawa da matakin raba kasashe zuwa rukunai daban daban bisa tunaninsu na siyasa, da fakewa da maganar dimokuradiyya a kokarin neman biyan bukatar kai.
- Sin Ta Shirya Harba Tauraron Dan Adam Na Queqiao-2
- Rukunin Farko Na Masu Yawon Bude Ido Da Suka Samu Bizar Tashar Shige Da Fice Ya Isa Xinjiang
Lin ya kara da cewa, a halin yanzu, abun da sassan kasa da kasa ke bukata ba wai haifar da rarrabuwar kai da sunan dimokuradiyya ba ne, maimakon haka ana fatan karfafa hadin gwiwa, da inganta dangantakar dimokuradiyya tsakanin sassan kasa da kasa bisa ka’idojin MDD.
Game da yadda wasu mutane daga bangaren yankin Taiwan na kasar Sin suka halarci taron kolin na dimokuradiyya kuwa, Lin Jian ya bayyana cewa, bangaren Sin na matukar adawa da yadda Koriya ta Kudu ta gayyaci hukumomin yankin Taiwan zuwa taron.
Ya ce kasar Sin daya tak ce a duniya, kana yankin Taiwan bangare ne na kasar Sin da ba za a iya balle shi ba. Kaza lika duk wani bangare na ketare, dake tsoma hannu cikin harkokin gidan Sin, ta hanyar nuna goyon baya ga manufar wai “’yancin kan Taiwan”, zai sha kaye.
Game da zartas da daftarin kudurin matakan kawar da tsoron Musulunci a babban taron MDD, Lin ya ce, Sin tana cikin kasashen da suka dauki nauyin tsara daftarin kudurin, inda ta yi maraba da zartas da daftarin kudurin. Ya ce bangaren Sin na ganin cewa, tayar da rikicin al’adu, da kuma kai hare-hare ga mabiya addinai, ba abun da za su haifar wa duniya illa rabuwar kawuna da kuma tashin hankali.
Game da matsayar Sin kan rikicin Rasha da Ukraine kuwa, Lin ya bayyana cewa, bangaren Sin na goyon bayan gudanar da taron tattaunawa na kasa da kasa, wanda bangarorin Rasha da Ukraine suka amince da shi. (Safiyah Ma)