Dakarun sojin Nijeriya sun ceto mutane 16 da aka yi garkuwa da su a kauyen Kajuru da ke Jihar Kaduna.
Sojojin sun kuma dakile wani yunkurin sace wasu mutane da ‘yan bindiga suka yi.
- BUƊA-BAKI [Falalarsa Da Lokacinsa] Na 3
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin: Kar A Fake Da Batun Dimokuradiyya Don Neman Biyan Bukatar Kai
“Rundunar sojin Nijeriya da aka tura Jihar Kaduna sun yi nasarar dakile wani yunkurin yin garkuwa da wasu mutane tare da kubutar da wasu mutane a unguwar Tantatu da ke karamar hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna,” in ji Daraktan yada labaran rundunar.
Manjo Janar Onyema Nwachukwu ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Litinin.
A cewarsa, sojojin sun samu nasara ne bayan samun bayanan sirri a daren ranar Lahadi, inda suka bibiyi maharan da suka yi awon gaba da wasu mutane a kauyen.
Sanarwar ta kara da cewa, “Da isar su wajen sai ‘yan ta’addar suka fara harbe-harbe, nan take suka yi musayar wuta tare da ceto mutane 16 da aka yi garkuwa da su.”
“Sojoji na ci gaba da bincike domin ceto sauran wadanda maharan suka sace.”
Babban hafsan sojin kasa Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya yaba wa sojojin bisa nasarar da suka samu.
Har wa yau, ya umarce su da su ci gaba da yaki da ‘yan ta’adda don samar da zaman lafiya a fadin kasar nan.