A yau Laraba, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum. Inda ya yi tsokaci game da bayanin da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yi a gun taron kolin dimokuradiyya na shugabanni, wanda a ciki ya zargi Sin da gurbata yanayin sadarwar duniya. Lin Jian ya bayyana cewa, bangaren Sin bai gamsu ba, kuma yana adawa da hakan. A sa’i daya kuma, ya shirya tattaunawa da bangaren Amurka.
Lin ya kara da cewa, Amurka ta habaka “dimokuradiyya ta hanyar aiwatar da mulkin kama karya”, karkashin “taron kolin dimokuradiyya”, wannan zargi karya ce zalla, har ila yau zargi Sin da yada labaran karya, shi ma labari ne maras tushe. Ya ce Amurka kasa ce mafi girma a fannin tsarawa, da kuma yada labaran karya, kuma al’ummun kasa da kasa sun san wannan kwarai da gaske.
- Sin Ta Harba Tauraron Dan Adam Na Queqiao-2
- Kasar Sin Ta Fitar Da Tsarin Amfani Da Kudin Yuan Ta Wayar Salula Domin Saukakawa Baki
Game da rikicin Falasdinu da Isra’ila, Lin Jian ya ce, tun bayan barkewar rikicin, bangaren Sin ya dade da himmatuwa wajen inganta tsagaita bude wuta, da kuma kare fararen hula.
A hannu guda, bagarorin da batun ya shafa sun yi matukar yaba wa bangaren Sin bisa matsayarta ta adalci, da kuma gudummawar da ta bayar wajen inganta tsagaita bude wuta, da kyautata yanayin jin kai da dai sauransu.
Game da rikicin Ukraine kuwa, Lin Jian ya bayyana cewa, abin da ya kamata a gaggauta yi a halin yanzu, shi ne inganta gudanar da tattaunawar siyasa don warware rikicin. (Safiyah Ma)