Yau da safe, an cimma nasarar aikin gwajin tafiyar jirgin kasa mai aiki da makamashin hydrogen, da reshen kamfanin Changchun na CRRC ya kera a birnin Changchun. Jirgin ya yi tafiya da saurin 160km kowace awa, wanda kuma ya cika dukkan ma’aunin da aka sanya kan irin wannan jirgi. Lamarin da ya alamta cewa, Sin ta samu sabon matsayi a wannan fanni.
Nasarar gwajin da Sin ta yi a wannan karo, za ta baiwa jirgin ingantaccen makamashin tafiya. Bisa alkaluman da aka bayar dangane da gwajin, an ce, matsakaicin yawan makamashin da jirgin ya kona a kowane kilomita ya kai 5 kh wato kilowat 5 a kowace awa, matakin dake sahun gaba a duniya.
Wani manazarci a wannan fanni ya bayyana cewa, gwajin da aka yi a wannan karo, ya zama tamkar wata muhimmiyar ishara a fannin amfani da makamashin hydrogen a fannin zirga-zirga a nan kasar Sin, wanda ya zama sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko wajen bunkasa ababen zirga-zirga masu jigilar hajoji. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp