Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya amince da a kara daukar karin kwararrun malaman makaranta guda 10,000.
El-Rufai ya amince da hakan ne ta hanyar hukumar karatun bai daya ta jihar (KADSUBEB).
- Matasan Arewa Sun Caccaki Babachir kan Sukar Takarar Musulmi da Musulmi
- ‘Yan Bindiga Da ‘Yan Kungiyar Ansaru Sun Yi Arangama Da Juna A Kaduna
Amincwar wacce ta ke kunshe a cikin sanarwar shugaban hukumar, Tijjani Abdullahi, ya fitar ta kara da cewa, hukumar ta bai wa Jami’ar KASU mallakar gwamnatin jihar da ta tsara tare da sauke manhajar sanar da daukar malaman daga ranar 21 ga watan Julin 2022.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, malaman da za a dauka, ana son su kasance masu shedar karatu na matakin NCE, babban digiri a fannin ilimi (B. Ed, B.A Ed, B. Sc, Bd, B.
A cewar sanarwar za a bude manhajar har zuwa sati biyu daga ranar 21 na watan Yuli zuwa ranar 5ga watan Agustan 2022.
Sanarwar ta ce, wadan suka nemi a dauke su zama a tantance su, inda kuma wadanda suka tsallake tantancewar za kirawo su don su zauna zana Jarrabawar gwaji ta kwamfuta a cibiyoyin Kaduna Zariya da Kafanchan.
A cewar sanarwar, sai wadanda suka samu kashi 75 a cikin dari na sakamakon jarrabawar ta kwamfuta za a gayyata zuwa tantancewa, inda kuma gwamatin za ta gayyace su don a tattauna da su baka da baka.
Sanarwar ta ce, wadanda suka samu nasara ana bukatar su zo takarardun na makaranta na ainahi da kuma na kwafi don yin tattaunarwar, inda za a bai wa masu tantancewar takardun na Foto Kwafin.