Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta cafke wani fursuna mai suna Kamala Lawal Abubakar dan shekara 33 da ke da zaune a Unguwar Sale a cikin karamar hukumar Danmusa wanda ta yi ammanar, ya na daya daga cikin fursunonin da suka arce daga gidan yarin Kuje da ke a babban birnin tarayyar Abuja.
Kakakin ‘yan sandan, SP Gambo Isa wanda ya holin Kamala Lawal ya sanar da cewa, sun kama shi a wata maboyar da ke a karamar hukumar ta Danmusa bayan bin diddigi.
- El-rufai Ya Amince Da Daukar Karin Malamai 10,000
- INEC Ta Mayar Da Martani Kan Zargin Birne Katukan Zabe A Gidan Wani Babban Dan Siyasa A Ribas
Ya sanar da cewa, a yayin da rundunar ta binciki Kamala Lawal, ya amsa cewa, ya arce ne daga gidan yarin Kuje da ke a Abuja, inda ya kara da cewa, an kuma kama shi dauke da ganyen da ake zargi na Tabawar Wiwi ne.
Kakakin ya bayyana cewa, indan rundunar ta kammala bincike a kansa, za ta mika shi zuwa ga mahukuntan gidan yarin na Kuje.