• English
  • Business News
Friday, May 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnan Bauchi Ya Yi Wa Fursunoni 96 Afuwa, Ya Bai Wa Kowa Kyautar Dubu 100

by Khalid Idris Doya
1 year ago
in Labarai
0
Gwamnan Bauchi Ya Yi Wa Fursunoni 96 Afuwa, Ya Bai Wa Kowa Kyautar Dubu 100
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya yi wa fursunoni 96 aka daure kan laifuka daban-daban a gidajen gyaran hali a jihar afuwa.

Gwamnan ya ba su kyautar Naira dubu 100 kowannensu da nufin su yi amfani da kudin wajen neman sana’ar da za su yi idan sun koma cikin al’umma.

  • Wuraren Kiwo: Fulani Sun Yi Murna Da Matakin Shugaban Kasa – Ngelzarma
  • Ɗaliban Jami’ar Jihar Nasarawa 2 Sun Mutu A Yayin Turmutsutsun Karɓar Abincin Tallafi

Gwamnan, wanda ya yi amfani da karfin ikon da doka sashe 212 (1) na kundin tsarin mulkin Nijeriya 1999 (da aka yi wa kwaskwarima) ya ba shi karkashin yin afuwa.

A yayin jawabinsa, gwamna ya ce, ya yi afuwar ne bisa shawarwari da kwamitin bayar da shawara kan yin afuwa na jihar ya yi, biyo bayan bibiyar zamantakewar fursunonin a gidan gyaran hali da kuma irin tuba da nadamar da suka yi kan laifukan da aka same su.

A cewar gwamnan, wadanda kwamitin ya yi la’akari da su wajen ganin an sake su sun hada da masu yawan shekaru, fursunoni masu dauke da cututtuka da ka iya yaduwa, da kuma wadanda aka yi musu daurin rai da rai amma sun shafe sama da shekaru sama da 10 a tsare tare da nuna nadama da ake da fatan za su kasance masu amfani idan suka koma cikin al’ummominsu.

Labarai Masu Nasaba

Masu Garkuwa Sun Nemi Miliyan ₦30 Don Sako Shugaban APC A Ondo

Dalilin Tsame Daya Cikin Uku Na Ma’aikatan Ƙasar Nan A Tsarin Sauye-sauyen Biyan Haraji – Czar

Sannan, gwamnan ya biya kudin tara da aka yanke wa wasu da nufin su samu fita daga daurewar da aka musu.

Sai dai a cewarsa, kwamitin ya yi fatali da bukatar wasu da suka aikata manyan laifuka, inda aka ki amincewa da fito da su.

Muhammad, ya hori wadanda ya sanya hannu aka sake su da su kasance mutane na kwarai kana su tabbatar ba su koma rayuwarsu na bayae da ya kai su ga shiga gidan yari ba.

“Kan halin da kasar nan ke ciki, kowane daga cikinku za a ba shi naira dubu 100, ina jan hankalinku da ku yi amfani da kudaden ta hanyar da ya dace. Kudin ba daga aljihuna ba ne, daga aljihun jiha ne.”

Gwamnan jihar ya bukaci babban jojin jihar da ta taka wa alkalai musamman alkalan da suke kananan kotuna da su daina yawan jibge mutane a gidajen yari kan wasu ‘yan laifukan da ba su kai a gungunta wa mutum rayuwarsa a gidan yari ba.

Shi kuma a jawabinsa, shugaban kwamitin yin afuwa kuma kwamishinan shari’a na Jihar Bauchi Hassan U. El-Yakub (SAN), ya ce gwamnan ya amince da fitar da kudi sama da naira miliyan bakwai domin biyan kudaden tara da kotuna suka yanke wa fursunonin kan laifukan da suka aikata.

Sannan, ya ce gwamnan ya kuma sake amincewa da fitar da wani kudi da yawan su ya kai Naira miliyan 13 da za a raba wa fursunonin da aka saki a matsayin tallafi da kudin mota domin su koma gidajensu domin ci gaba da kasance masu amfani a cikin al’umma.

“Kwamitin bayar da shawara kan afuwa ya amshi bukata daga wajen fursunoni 106 da suke rokon yafiyar gwamna. Amma kwamitinmu ya kai ziyara zuwa gidajen yari da suke Bauchi, Alkaleri, Azare, Bogoro, Burra, Darazo, Ningi, Zaki, Gamawa, Misau, Shira, Toro, Tafawa Balewa da Jama’are, inda aka karshe kwamitin ya amince da bukatar fursunoni 96 kuma cikin tausayawar gwamna ana gabatar masa ya amince.”

A nasu jawaban daban-daban kwanturolan hukumar kula da gidan yari a jihar Bauchi, Ali Bajoga, kwamishinan ‘yansanda na Jihar Bauchi Auwal Musa da sauran sun jinjina wa gwamnan bisa yin afuwar, sun kuma nuna hakan zai kara rage cunkoson da ake fama da shi a gidajen gyaran hali a jihar.

Wasu daga cikin fursunonin da aka sake su, sun nuna godiyarsu tare da daukar alkawarin ba za su sake komawa rayuwarsu ta baya ba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Hedkwatar CDC Ta Afirka Ta Samu Yabo A Matsayin Babban Sakamakon Hadin Gwiwar BRI

Next Post

Ku Yi Amanna Da Tinubu, Matsalolin Zu Su Zo Karshe, inji Ministan Yaɗa Labarai

Related

Masu Garkuwa Sun Nemi Miliyan ₦30 Don Sako Shugaban APC A Ondo
Tsaro

Masu Garkuwa Sun Nemi Miliyan ₦30 Don Sako Shugaban APC A Ondo

59 minutes ago
Dalilin Tsame Daya Cikin Uku Na Ma’aikatan Ƙasar Nan A Tsarin Sauye-sauyen Biyan Haraji – Czar
Labarai

Dalilin Tsame Daya Cikin Uku Na Ma’aikatan Ƙasar Nan A Tsarin Sauye-sauyen Biyan Haraji – Czar

2 hours ago
Rashin Tsaro Da Raba Wa Manoma Kayan Aiki Kan Lokaci Na Baraza Ga Wadata Kasa Da Abinci
Labarai

Rashin Tsaro Da Raba Wa Manoma Kayan Aiki Kan Lokaci Na Baraza Ga Wadata Kasa Da Abinci

6 hours ago
Faɗuwar Farashi: Masu Ɓoye Abinci Don Ya Yi Tsada, Asara Kawai Suke Ƙirgawa , In Ji BUA
Manyan Labarai

Faɗuwar Farashi: Masu Ɓoye Abinci Don Ya Yi Tsada, Asara Kawai Suke Ƙirgawa , In Ji BUA

14 hours ago
Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Dokar Karɓa-karɓa A Kujerar Shugaban Ƙasa A Tsakanin Shiyyoyin Nijeriya
Labarai

Majalisar Wakilai Za Ta Binciki Yadda Aka Samu Mummunan Sakamakon Jarabawar UTME 2025

16 hours ago
HOTO: Ofishin Tsohon Shugaban Kasa Shagari Bayan Shekara 42
Labarai

HOTO: Ofishin Tsohon Shugaban Kasa Shagari Bayan Shekara 42

18 hours ago
Next Post
Ku Yi Amanna Da Tinubu, Matsalolin Zu Su Zo Karshe, inji Ministan Yaɗa Labarai

Ku Yi Amanna Da Tinubu, Matsalolin Zu Su Zo Karshe, inji Ministan Yaɗa Labarai

LABARAI MASU NASABA

Masu Garkuwa Sun Nemi Miliyan ₦30 Don Sako Shugaban APC A Ondo

Masu Garkuwa Sun Nemi Miliyan ₦30 Don Sako Shugaban APC A Ondo

May 16, 2025
Dalilin Tsame Daya Cikin Uku Na Ma’aikatan Ƙasar Nan A Tsarin Sauye-sauyen Biyan Haraji – Czar

Dalilin Tsame Daya Cikin Uku Na Ma’aikatan Ƙasar Nan A Tsarin Sauye-sauyen Biyan Haraji – Czar

May 16, 2025
Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mahajjaci

Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mahajjaci

May 16, 2025
Tinubu Ya Kira Taron Manyan Kafafen Yada Labarai Kan Samar Da Wadataccen Abinci

Tinubu Ya Kira Taron Manyan Kafafen Yada Labarai Kan Samar Da Wadataccen Abinci

May 16, 2025
Abin  Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (1)

Abin  Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (1)

May 16, 2025
Rashin Tsaro Da Raba Wa Manoma Kayan Aiki Kan Lokaci Na Baraza Ga Wadata Kasa Da Abinci

Rashin Tsaro Da Raba Wa Manoma Kayan Aiki Kan Lokaci Na Baraza Ga Wadata Kasa Da Abinci

May 16, 2025
Kasar Sin Ta Yanke Shawarar Hana Taiwan Halartar Babban Taron WHO Na Bana

Kasar Sin Ta Yanke Shawarar Hana Taiwan Halartar Babban Taron WHO Na Bana

May 15, 2025
Faɗuwar Farashi: Masu Ɓoye Abinci Don Ya Yi Tsada, Asara Kawai Suke Ƙirgawa , In Ji BUA

Faɗuwar Farashi: Masu Ɓoye Abinci Don Ya Yi Tsada, Asara Kawai Suke Ƙirgawa , In Ji BUA

May 15, 2025
Sin Ta Bukaci Amurka Ta Dakatar Da Harajin Sashe Na 232

Sin Ta Bukaci Amurka Ta Dakatar Da Harajin Sashe Na 232

May 15, 2025
Xi Ya Taya Shugaban Togo Murnar Karbar Ragamar Shugabanci

Xi Ya Taya Shugaban Togo Murnar Karbar Ragamar Shugabanci

May 15, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.