Da yammacin yau Litinin 25 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Nauru, David Ranibok Adeang, wanda yanzu haka ke ziyara a kasar Sin, a babban dakin taron jama’a.
Kafin shawarwarin kuma, shugaba Xi ya shirya bikin maraba ga shugaba Adeang.
Bisa gayyatar da shugaba Xi ya yi masa ne, shugaba Adeang yake ziyarar aiki a kasar ta Sin daga ranar 24 zuwa 29 ga wata. (Mai fassara: Bilkisu Xin)