Ministan ma’aikatar kudi na kasar Sin Lan Fo’an, ya zayyana manyan matakan da ma’aikatarsa za ta aiwatar domin ingiza ci gaba mai inganci a shekarar nan ta 2024.
Lan, wanda ya yi bitar matakan yayin jawabin da ya gabatar, a wani dandali na tattaunawa game da ci gaban kasar Sin a shekarar bana, wanda aka bude jiya Lahadi a nan birnin Beijing, ya ce ma’aikatarsa za ta sa kaimi ga bunkasa sabbin matakan sarrafa hajoji, da kara adadin kudaden tallafawa kirkire-kirkire, da daga darajar masana’antu, da kirkirar sabbin masana’antu don gaba.
- Amurka: Mai Shafawa Sauran Kasashe Bakin Fenti
- Xi Jinping Ya Yi Shawarwari Tare Da Takwaransa Na Kasar Nauru
Ministan ya kara da cewa, ma’aikatarsa za ta mayar da hankali ga fadada jari masu samar da riba, da ingiza ikon sayayya, wanda zai karfafa bukatun cikin gida don bunkasa ci gaban tattalin arziki.
Har ila yau, ma’aikatar kudin ta Sin, za ta tallafawa ayyukan sabunta kayayyakin aiki, da cinikayyar hajojin amfanin yau da kullum ta hanyar musayar tsofaffi da sababbi da yin cikon kudi. Ya ce ma’aikatar za ta baiwa dukkanin sana’o’i damar cin gajiyar rangwamen haraji, da sayayya daga lalitar gwamnati. (Saminu Alhassan)