Za a iya sakin dan wasan kwallon kafa na duniya, Dani Alves daga gidan yari bayan ya biya kudin belin Yuro miliyan 1 (£ 853,000) da wata kotu a kasar Sifaniya ta yanke masa bayan ta sameshi da laifin fyade a watan Fabrairun 2024.
An yanke wa Alves hukuncin daurin shekaru hudu da rabi a gidan yari a watan da ya gabata, bayan da wata kotu ta same shi da laifin yi wa wata mata fyade a wani gidan rawa na Barcelona a shekarar 2022.
- Barcelona Ta Kai Matakin Kwata Final A Gasar Zakarun Turai Bayan Shekara 4
- FIFA Ta Fara Bincike Kan Sumbata Da Rubiales Ya Yi Wa ‘Yar Wasan Spain
A ranar Litinin, wata kotu a Sifaniya ta baiwa tsohon dan kwallon Barcelona kuma dan kasar Brazil izinin barin gidan yari har zuwa lokacin da zai daukaka kara, an tsare Alves mai shekaru 40 a gidan yari tun watan Janairun 2023.
Sharuddan sakin nasa sun hada da bayar da fasfo dinsa na Brazil da na Sifaniya, don haka ba zai iya barin Sifaniya ba, kuma dole ne ya bayyana a gaban kotu a kowane mako.
Alves ya yi mabanbantan maganganu a lokuta da dama, inda a farko ya musanta cewa ya san wacce tayi kararsa a kotu amma daga baya ya ce ya hadu da ita a wani bandaki amma babu abin da ya shiga tsakaninsu.