Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa tuni jami’an tsaro suka yi wa fitaccen malamin nan, Sheikh Ahmad Gumi, tambayoyi kan kalamansa na baya-bayan nan kan ‘yan bindiga a Nijeriya.
Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai na Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja a ranar Litinin.
- ‘Yan Bindiga: Jami’an Tsaro Sun Gayyaci Sheikh Gumi Domin Amsa Tambayoyi
- Xi Jinping Ya Yi Shawarwari Tare Da Takwaransa Na Kasar Nauru
A cewar ministan: “Gwamnati za ta yi komai don samun duk wani bayani da ake buƙata don magance matsalolinmu, jami’an tsaro suna nan suna aiki.
“Sheikh Gumi ko wasu mutane ba su fi ƙarfin doka ba. Idan yana da wasu shawarwari ƙwarara da suka dace kuma masu inganci da jami’an tsaro za su yi aiki da su, to za su ɗauka, amma idan suna tunanin yana yin wasu kalamai ne na ganganci, za a tsawata masa. Babu wanda ya fi ƙarfin doka.”
Idris ya ƙara cewa, “Bari in faɗa maku wani abu, ina sane da cewa, jami’an tsaro sun gayyace shi don amsa tambayoyi.
“Idan ka yi wani kalami musamman kan tsaron ƙasar mu, ya zama wajibi jami’an tsaron ƙasarmu su yi ƙarin tunani kan hakan kuma dama suna yin hakan. Babu wanda ya fi ƙarfin doka.”