• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasar Sin Ta Kasance Ja Gaba Wajen Lalubowa Duniya Sabbin Damarmakin Ci Gaba

by CGTN Hausa
2 years ago
sin

An kammala taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa kan ci gaban kasar Sin a jiya Litinin, inda mahalarta ke ganin  cewa ta hanyar ci gaba mai inganci da bude kofarta, ba kokarin samun ci gaba bisa kuzarinta da boyayyen karfinta kadai Sin ke yi ba, har ma da taka rawar gani wajen gaggauta ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya.

A ko da yaushe Sin kan furta cewa, gabanta ba barazana ba ce, dama ce. A ganina, tabbas haka batun yake domin duk wani ci gaban da Sin take samu, tana gabatar da shi ga duniya domin samar da sabbin dabaru.

  • Sin Ta Taka Rawar Gani Ga Bunkasuwar Tattalin Arzikin Duniya
  • Kasar Sin Na Maraba Da Abokai ‘Yan Kasuwa Daga Kasashe Daban Daban Da Su Ci Gaba Da Zuba Jari A Kasar 

Kamar yadda a kullum kasar ke zama abun misali ko koyi ga sauran kasashe, duk wani ci gaban da Sin ta samu, zai kasance tamkar zaburarwa ne ga kasashen duniya na son koyi da ita domin kada a bar su a baya. Za mu iya cewa, kasar Sin ta kasance jagora kuma ja gaba, wajen lalubowa duniya sabbin hanyoyin samun ci gaba cikin lumana da ma shawo kan matsaloli.

Ci gaban Sin zai ci gaba da kasancewa tabbaci ga sauran kasashe musamman kasashe masu tasowa cewa, su ma za su iya samun ci gaban tattalin arziki da kyautatuwar zamantakewa kamar na Sin, idan suka nace, suka kuma zabarwa kansu manufofin da suka dace da yanayinsu, kana suka sanya kishin kasa da ruhin sadaukarwa a zukatansu kamar yadda Sin ta yi.

Mun ga yadda al’amura suka tsaya cik a lokacin da annobar COVID-19 ta aukawa kasar Sin. Mun shaida yadda aka samu tsaikon samun kayayyaki da hauhawar farashinsu saboda tasirin COVID-19 a kasar Sin. To kamar yadda aka ga mummunan tasiri a wancan lokaci, haka ci gaban kasar Sin zai haifar da kyakkyawan tasiri ga duniya.

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza

An Yi Tafiye-tafiye Miliyan 16.34 Da Suka Shafi Shiga Da Fita Daga Kasar Sin Yayin Hutun Kwanaki 8 Na Kasar 

Idan muka duba bangarori kamar na fasahohin zamani, kowa ya san kasar Sin ce ja gaba a wannan fanni, kuma tana samar da sabbin fasahohi kusan kullum a bangarori daban daban da suka shafi rayuwar jama’a da ayyukansu. Misali yadda take ingantawa da zamanintar da aikin gona, abu ne da zai taka rawar gani wajen samar da wadatar abinci a duniya. Motoci masu amfani da lantarki da Sin take samarwa, za su yi matukar amfani wajen rage dogaro da man fetur, da rage dumamar yanayi don samar da kyakkyawan muhallin rayuwa ga bil adama. Haka ma, bude kofarta da take kara yi, wata dama ce ga kamfanonin kasashen waje na cin gajiyar ci gaban kasar da babbar kasuwar da take da ita.

Don haka abun yi shi ne, kasashen dake neman ci gaba da gaske, su daura damara, su shirya, domin kasar Sin za ta lalubo musu sabbin hanyoyin da za su kara samun alfanu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza
Daga Birnin Sin

Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza

October 9, 2025
An Yi Tafiye-tafiye Miliyan 16.34 Da Suka Shafi Shiga Da Fita Daga Kasar Sin Yayin Hutun Kwanaki 8 Na Kasar 
Daga Birnin Sin

An Yi Tafiye-tafiye Miliyan 16.34 Da Suka Shafi Shiga Da Fita Daga Kasar Sin Yayin Hutun Kwanaki 8 Na Kasar 

October 9, 2025
Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar
Daga Birnin Sin

Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar

October 9, 2025
Next Post
BRI

Hadin Gwiwar Shawarar BRI Tsakanin Habasha Da Sin Zai Kara Bunkasa Rayuwar Al’ummun Habasha

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama Motar Hilux Ɗin Da Aka Sace A Kano A Hanyar Zuwa Nijar

‘Yansanda Sun Kama Motar Hilux Ɗin Da Aka Sace A Kano A Hanyar Zuwa Nijar

October 9, 2025
Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza

Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza

October 9, 2025
TCN

Jami’an Tsaro Sun Cafke Ɓarayin Kayayyakin Turakun Wutar Lantarki Na Hanyar Mando Zuwa Jos

October 9, 2025
An Yi Tafiye-tafiye Miliyan 16.34 Da Suka Shafi Shiga Da Fita Daga Kasar Sin Yayin Hutun Kwanaki 8 Na Kasar 

An Yi Tafiye-tafiye Miliyan 16.34 Da Suka Shafi Shiga Da Fita Daga Kasar Sin Yayin Hutun Kwanaki 8 Na Kasar 

October 9, 2025
Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

October 9, 2025
Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar

Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar

October 9, 2025
Fursunoni Ba Za Su Samu Damar Kada Kuri’a Ba A Zaben 2023 – INEC

Batun Umarnin Kotu Na Kama Tsohon Shugaban INEC Ƙage Ne Kawai – Shugaban Jam’iyyar AA 

October 9, 2025
An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

October 9, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

October 9, 2025
Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

October 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.