• English
  • Business News
Wednesday, October 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

A Kawo Dauki Don Magance Tsadar Kudin Zuwa Aikin Hajjin Bana

by Abubakar Ibrahim
2 years ago
hajjin 2024

A kowace shekara, al’ummar Musulmi suna gudanar da aikin Hajji domin cika daya daga cikin shikashikan addininsu guda biyar. Abu ne wanda kowane Musulmi ke son cimmawa, akalla sau daya a rayuwarsa, yayin da kuma wani mai kumbar susa yake da burin ya sake komawa ya kara yi. Duk da haka, wanda ke da hali ne kadai aka wajabta wa yin wannan tafiya zuwa kasa mai tsarki don sauke farali.

A Nijeriya, tuni shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin shekarar 2024 suka kankama. Sai dai kuma ana ta samun wani babban kalubale, musamman na kudin tafiya aikin na maniyyata. Duk da kokarin da Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) take yi na ganin an shawo kan tsadar kudin tafiya Hajjin bana, farashin ya yi tashin gwauron zabi wanda ba a taba ganin irinsa a baya ba. Lamarin ya jefa maniyyata cikin halin kaka-ni-ka-yi da tsananin rudani.

  • IFAD Da Gwamnatin Tarayya Sun Yi Hadaka Don Bunkasa Aikin Noma A Arewa
  • Sin Da EU Sun Gudanar Da Taron Tattaunawa Domin Inganta Musaya Tsakanin Jama’arsu

Duk da ce-ce-ku-cen da ake yi game da karin kudin, matsalar ta samo asali ne daga wasu manyan abubuwa guda biyu — su ne hauhawar farashin Dalar Amurka da kuma jinkiri ko kin biyan kudin aikin Hajji kan lokaci daga maniyyata.

Idan an tuna, tun da farko sai da hukumar NAHCON ta kayyade mafi karancin kudin ajiya na aikin Hajjin bana a kan naira miliyan hudu da rabi (N4.5m), aka ce za a fadi farashi na karshe bisa la’akari da farashin Dala a lokacin da za a kammala lissafa kudin. Saboda sauyin farashin Dala, ya zama tilas hukumar ta yi kari kan farashin ta na farko.
Karin da aka yi dai sakamakon faduwar darajar Naira ne. Duk da kokarin da Shugaban NAHCON, Malam Jalal Ahmad Arabi ya yi na ganin farashin zuwa aikin Hajjin bana bai canza ba, an bukaci maniyyata da su biya naira 4,899,000 ga wadanda suka fito daga Kudu, wadanda suka fito daga Arewa kuma naira 4,699,000, sannan naira 4,679,000 ga wadanda suka fito daga yankin Yola da Maiduguri.

Matsalar da Nijeriya ta kwashe watanni tana fama da ita na canjin kudaden waje ya sa tilas hukumar ta nemi wadanda suka biya kudin ajiya na kimanin naira miliyan 4.9 da su cika naira 1,918,032.91, daidai da farashin kudaden waje na yanzu. Hakan ya sa adadin kudin da masu niyyar zuwa aikin Hajjin za su biya ya zama naira miliyan 6.8 ga ‘yan ajiya. Su kuwa sababbin masu son biyan kudin za su biya naira 8,225,464.74 daga maniyyata daga Arewa, yayin da maniyyatan Kudu za su biya naira 8,454,464.73. Kuma hukumar ta ce ana bukatar a kammala biyan wadannan kudaden kafin karfe 11:59 na dare a ranar 28 ga Maris, 2024.

LABARAI MASU NASABA

Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025 Na Jaridar Leadership: Dauda Lawal

Hukumar NAHCON ta yi kokari da dama wajen ganin maniyyata sun samu saukin farashi a bana. Misali, a farkon wannan shekarar shugaban hukumar ya jagoranci tawagar jami’ansa zuwa kasar Saudiyya inda suka tattauna da masu gidajen haya da otal-otal da motocin haya a garuruwan Makka da Madina da Masha’ir don su rage kudi ga maniyyatan Nijeriya, kuma sun samu matukar nasarar hakan. Tattaunawar ta haifar da raguwar farashin jirgi da masauki da sauran su. In da ba domin zuwan da suka yi ba, to da kudin zuwa Hajji da ake magana yanzu ya zarta haka.

Duk da matakan ragin kudaden da NAHCON ta dauka da suka hada da neman tallafin gwamnatocin jihohi da masu hannu da shuni ga alhazan su, da kuma shiga tsakani da Gwamnatin Tarayya ta yi, gazawar maniyyatan wajen cika wa’adin da aka bayar na biyan kudin aikin Hajjin da aka kara shi ma ya haifar da karin kudin zuwa aikin Hajjin bana. Rashin biyan cikakken kudi a kan lokacin da aka tsara ya haifar da tsawaita wa’adin, kuma yayin da aka tsawaita wa’adin, farashin kudaden waje na hauhawa. Hakan ne ya sa kudin aikin Hajjin ya karu.

Ba shakka, karin kudin aikin Hajji ya zama babban kalubale ga maniyyatan Nijeriya a bana. A halin da ake ciki, akwai alamun da yawa daga cikin maniyyatan da suka biya kudin ajiya ba za su iya biyan cikon naira miliyan 1.9 da ake bukata ba, yayin da su kuma sababbin biya da yawansu sai dai ido, musamman a cikin takaitaccen wa’adin da NAHCON ta bayar. Hakan zai sa maniyyata su rasa damar zuwa Saudiyya gaba daya.

Don haka, ya zama wajibi ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da masu hannu da shuni da su shigo cikin al’amarin, su ba da tallafi don sassauta nauyin da ke kan maniyyatan, tare da daukar matakan da za su sa maniyyata na nan gaba su samu saukin yin wannan tafiya mai alfarma. Kada a nade hannu a zuwa wa matsalar ido, musamman a cikin wannan takaitaccen lokaci.

* Abubakar Ibrahim dalibin digiri na biyu ne a Sashen Koyon Aikin Jarida a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi
Manyan Labarai

Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi

October 22, 2025
Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025 Na Jaridar Leadership: Dauda Lawal
Labarai

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025 Na Jaridar Leadership: Dauda Lawal

October 22, 2025
Shugaban NAHCON Ya Musanta Zargin Tsare Ɗan Jarida Da Aikata Cin Hanci
Labarai

Shugaban NAHCON Ya Musanta Zargin Tsare Ɗan Jarida Da Aikata Cin Hanci

October 22, 2025
Next Post

Abin Da Masu Hannu Da Shuni Ya Kamata Su Rika Yi A Kan Rabon Zakkah

LABARAI MASU NASABA

Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi

Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi

October 22, 2025
Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025 Na Jaridar Leadership: Dauda Lawal

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025 Na Jaridar Leadership: Dauda Lawal

October 22, 2025
Shugaban NAHCON Ya Musanta Zargin Tsare Ɗan Jarida Da Aikata Cin Hanci

Shugaban NAHCON Ya Musanta Zargin Tsare Ɗan Jarida Da Aikata Cin Hanci

October 22, 2025
Babaganaru Ya Zama Sabon Kocin Kano Pillars

Babaganaru Ya Zama Sabon Kocin Kano Pillars

October 22, 2025
ADC Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Amfani da Zargin Juyin Mulki Wajen Yaƙar ‘Yan Adawa

ADC Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Amfani da Zargin Juyin Mulki Wajen Yaƙar ‘Yan Adawa

October 22, 2025
ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta

ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta

October 22, 2025
Rashin Abinci Mai Gina Jiki Barazana Ce Ga Lafiyar Al’umma – Gwamna Lawal

Rashin Abinci Mai Gina Jiki Barazana Ce Ga Lafiyar Al’umma – Gwamna Lawal

October 22, 2025
Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe

Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe

October 22, 2025
Gobara Ta Tashi A Kasuwar Alaba Da Ke Legas

Gobara Ta Tashi A Kasuwar Alaba Da Ke Legas

October 22, 2025
Gwamnoni Sun Yi Ta’aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Fashewar Tankar Mai A Neja

Gwamnoni Sun Yi Ta’aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Fashewar Tankar Mai A Neja

October 22, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.