Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya gana da takwaransa na Benin Shegun Adjadi Bakari, a jiya Alhamis a birnin Beijing, inda suka tattauna hanyoyin kara bunkasa dangantakar kasashen su.
Yayin tattaunawar jami’an, Wang Yi wanda kuma mamba ne na zaunannen kwamitin hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, ya ce Sin a shirye take ta bunkasa alakar dake tsakaninta da Benin, karkashin muhimman kudurorin da shugabannin kasashen biyu suka cimma.
- Ministan Lafiya Na Yunkurin Samar Da Sabon Shirin Taskace Bayanan Majinyata
- Xi Jinping Ya Taya Bassirou Diomaye Faye Murnar Zama Shugaban Senegal
Wang Yi ya kara da cewa, Sin za ta goyi bayan hanyar bunkasa kai da Benin ta zaba da kanta daidai da yanayin da kasar ke ciki. Kaza lika, za ta kasance abokiya ta hakika, wadda Benin za ta iya dogaro da ita a fannin ingiza zamanantarwa.
A nasa bangare kuwa, mista Bakari cewa ya yi Benin na goyon bayan manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, kuma kasarsa za ta shiga a dama da ita a dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka dake tafe nan gaba a bana, kana za ta bayar da gudummawar da ta kamata a fannin bunkasa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka. (Saminu Alhassan)