Jam’iyyar PDP na Jihar Osun ta yi zargin an kama mata mambobi har guda 25, wanda lamarin ya haddasa musayar kalamai tsakaninta da APC a jihar.
PDP ta yi wannan zargin ne a cikin wata sanarwa da shugaban jam’iyyar na Jihar Osun, Sunday Bisi ya fitar. Ya yi ikirarin cewa tawagar jami’an tsaro na Abuja ne suka kama masu mambobin.
- Ministan Lafiya Na Yunkurin Samar Da Sabon Shirin Taskace Bayanan Majinyata
- Kasar Sin Na Bayar Da Cikakken Goyon-Baya Ga Pakistan Wajen Yakar Ta’addanci
Haka kuma Bisi ya zirgi jami’an tsaro da kai wannan samame ba tare da sanarwa ba. Ya ce daga cikin wadanda aka kama sun hada da masu bayar da shawara guda 4 da shugabanni 5 da sauran mambobi 15, wadanda aka kama kuma aka tafi da su zuwa Abuja.
Bisi ya ce tun ranar Alhamis wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC suka bayyana shirin kama mambobin PDP da wasu jami’an gwamnatin Osun, wanda suke amfani da gwamnatin tarayya wajen cin zarafin shugabannin jam’iyyarsu ta PDP.
Ya bukaci rundunar ‘yansanda da jami’an tsaro na farin kaya da su kaurace wa hadawa harkokin siyasa da suke ke jefa su a ciki saboda sun kashe samun nasara kan zabe.
A nasa martanin, shugaban jam’iyyar APC a jihar, Tajudeen Lawal ya bayyana cewa wannan zargin bai da tushe ballantana makama.
Lawal ya ce jam’iyyar PDP a Jihar Osun tana kokarin kaucewa amsar tambayoyi ne kan kwangilolin da gwamnatin Adeleke ta bayar ba bisa ka’ida ba.