Yanzu haka ana gudanar da taron shekara shekara na dandalin tattaunawa tsakanin kasashen Asiya na Boao na 2024, a garin Boao na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin. Shugaban kasar Nauru David Ranibok Adeang wanda ke halartar taron ya zanta da wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na Sin na CMG a ranar Laraba 27 ga wata, inda ya jinjinawa nasarorin da Sin ta cimma a fannin kawar da talauci, yana mai cewa, Sin tana da gogewa a fannin cimma nasarori masu yawa, wadanda sauran kasashen duniya za su iya koyo.
Wannan shi ne karo na farko da Shugaba Adeang ya ziyarci Sin, tun bayan da kasashen biyu suka maido da huldar diplomassiya tsakaninsu a ranar 24 ga watan Janairun bana.
- Xi Jinping Ya Taya Bassirou Diomaye Faye Murnar Zama Shugaban Senegal
- Kungiyar Tsoffin Jami’an NIS Ta Yaba Da Nadin Sabuwar Kwanturola Janar Ta Hukumar
Shugaba Adeang ya kara da cewa, ya kamata kasa da kasa su yi taka tsantsan yayin da suke tafiyar da harkokin kasa, daidaita dangantakar dake tsakaninsu, da kuma sauke nauyin dake bisa wuyansu tare, a kokarin magance kawo illoli ga juna.
Ya ce jigon taron shekara shekara na dandalin Boao na bana ya baiwa mutane sha’awa, wanda ya karfafa wa shugabannin kasashen duniya gwiwa, wajen rungumar akidun kaucewa zalunci, da wanzar da zaman lafiya, da kuma samun ci gaba tare, lamarin da zai amfana wa duk duniya.
Haka zakila, Shugaba Adeang ya ce, aikin rika samun saurin bunkasar tattalin arziki a jerin shekaru ba abu ne mai sauki ba ga wata kasa. Amma Sin ba ma kawai ta samu ci gaban tattalin arzikinta cikin goman shekaru a jere ba, har ma ta taimakawa daruruwan miliyoyi jama’a wajen fita daga kangin talauci. Ya kamata kasashen duniya musamman ma kasashe masu tasowa su koyi yadda Sin ta samu irin wadannan nasarori, bisa yanayin da suke ciki. (Safiyah Ma)