Gwamnatin jihar Bauchi a karkashin jagorancin Sanata Bala Muhammad ta tallafa wajen biyan kaso hamsin cikin dari na karin kudin kujerar aikin hajji da hukumar kula da alhazai ta yi ga maniyyata aikin hajjin bana.
Inda gwamnan ya sanar da biyan kashi hamsin cikin naira miliyan 1,918,000 na karin kudin hajji da NAHCON ta yi kan kowace kujerar zuwa aikin hajji. Maniyyata 1652 ne za su amfana, inda kowani maniyyaci zai ci gajiyar tallafin naira dubu N950, 000.
- An Kammala Taron Dandalin Boao Na 2024 Cikin Nasara
- Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Benin Domin Tattauna Hanyoyin Karfafa Dangantakar Kasashensu
Idan za a tuna dai, hukumar kula da jin dadin alhazai ta kasa NAHCON, ta sanar da cewa, kowani maniyyacin da ya biya kudin kujera da niyyar sauke farali zuwa kasa mai tsarki a watannin baya, yanzu zai sake biyan naira miliyan 1.9 domin ya cike naira miliyan 4.9 da suka biya da zai zama sama da naira miliyan shida a matsayin kudin kujerar aikin hajjin 2024.
Kwamishinan kula da harkokin addinai na jihar Bauchi, Hon. Yakubu Hamza shi ne ya sanar da matakin karin a wani taron manema labarai da ya kira a ranar Juma’a, inda ya ce, adadin naira N1, 584, 268, 000 ne gwamnan ya biya wajen tallafa wa karin kudin kujerar ga alhazan.
Hamza ya ce wannan abun yabawa ne lura da cewa kudin da aka kara wa alhazan ba kowa zai iya cikawa ba, inda ya shawarci maniyyatan da su nemo rabin kudin su cika domin amfana da tallafin rabi da gwamnan ya musu.
Ya kara da cewa, wannan tallafin kaso hamsin ya hada har da alhazan da gwamnatin jihar ta dauki nauyin aikin hajjinsu, ya ce idan aka hada dukkanin alhazan da suka biya kudin kujera da fari da wanda da gwamnatin jihar ta biya musu, tallafin da gwamnan ya kara zai kai naira N2, 196, 110, 000.
Shi kuma a nasa bangaren, shugaban hukumar kula da jin dadin alhazai na jihar Bauchi Imam Abdurrahman Ibrahim Idris, ya ce, a kowani lokaci gwamna Bala na maida hankali wajen kyautata jin dadi da walwalar maniyyatan jihar.
Ya ce akwai wasu tsare-tsare da aka yi da za su tabbatar da kyautatawa maniyyata tare da jin dadinsu a yayin gudanar da aikin hajji na bana.