Gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola, ya sha kaye a zabensa na sake tsayawa takara karo na biyu a hannun dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP, Sanata Ademola Adeleke.
A baya LEADERSHIP ta kawo muku rahoto cewa, Adeleke ya lashe kananan hukumomi 17 daga cikin 30 na jihar yayin da gwamna mai ci kuma dan takarar jam’iyyar APC, Gboyega Oyetola, ya lashe sauran kananan hukumomi 13.
- Osun: Za Mu Karbi Kudin ‘Yan Takara Mu Zabi Wanda Muke So – Ma Su Kada Kuri’a
- Zaben Osun: ‘Yan Nijeriya Na Kallon Mu – Mahmoud Ga Ma’aikatan INEC
Yayin da Adeleke ya samu kuri’u 403,371 a zaben gwamnan jihar Osun da aka gudanar a ranar Asabar 16 ga Yuli, 2022, Gwamna Oyetola ya samu kuri’u 375,027.
Da yake sanar da sakamakon karshe a safiyar Lahadi, babban jami’in zabe na INEC, Farfesa Oluwatoyin Temitayo Ogundipe, wanda shi ne mataimakin shugaban jami’ar Legas (UNILAG), ya ayyana Ademola a matsayin wanda aka zaba saboda ya samu mafi yawan kuri’u.
LEADERSHIP ta tabbatar da cewa duk da cewa akwai ‘yan takara 15 da suka fafata a zaben gwamnan Osun, Oyetola na APC da Adeleke na PDP su ne suka fafata a zaben.