Ma’aikatar kula da harkokin addini ta Jihar Kebbi, ta amince da murabus din babban limamin masallacin juma’a da ke Wala a Birnin Kebbi, Sheikh Rufa’i Ibrahim Bashar.
Ma’aikatar ta kuma amince da nadin mataimakin limamin masallacin, Malam Mammam Nata’ala Yahaya, domin ya zama Limamin Masallacin a matsayin mai riko.
- Me Ya Fi Ci Wa Samari Da ‘Yan Mata Tuwo A Kwarya Game Da ‘Ramadan Basket’?
- Idan Aka Fatattaki ‘Yan Ta’adda Daga Zamfara Duk Arewa Za Mu Samu Sauki – Gwamna Dauda
Kwamishinan ma’aikatar, Muhammad Sani Aliyu, ya bukaci Majalisar Masarautar Gwandu da ta nada babban Limamin Masallacin Wala na Juma’a.
Aliyu, ya ce tsohon limamin ya yi murabus daga mukamin ne bisa kashin kansa wanda karamar hukumar Birnin Kebbi ta amince
Kwamishinan ya karyata rade-radin da ake cewa Sheikh Rufa’i Ibrahim Bashar ya bar matsayinsa kan batun kudi.
“Gwamna Nasir Idris ya bayar da tallafin kudi ga limaman masallatan juma’a na jihar domin taimaka musu wajen rage wahalhalun da tattalin arzikin kasar nan ke ciki a halin yanzu da kuma taimakon na kusa da su.
“Gwamnati ba ta taba samun wani rahoto na nuna kaffa-kaffa wajen rabon kudaden ba, don haka zargin rage kudaden da mukarrabansa ke yi wa tsohon babban limamin, ba gaskiya ba ne,” in ji shi.
A nasa gudunmuwar kwamishinan yada labarai da al’adu, Alhaji Yakubu Ahmad Birnin Kebbi, ya yi watsi da batun siyasa a cikin labarin tsohon babban limamin.
“Muna cikin tsarin dimokuradiyya, Limamai suna da akidar siyasa daban da gwamnatin da ke mulki ba tare da cin zarafi ko tsangwama ba, Gwamnanmu duk yana karba, duk dan jihar Kebbi masoyinsa ne.
“Wadanda ke tafka kura-kurai a siyasance a matsayin dalilin murabus dinsa sun yi kuskure. Sheikh Rufa’i Ibrahim Bashar Wala ya ajiye mukaminsa bisa son ransa,” in ji Kwamishinan.