Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, hukumomi da dama na kasar Sin sun gabatar da jerin matakan fadada bude kofa ga kasashen waje, wadanda suke shafar samar da hidimomi a tsakanin kasa da kasa, da raya tattalin arzikin sadarwa a tsakanin kasashe, da hada-hadar kudi da sauransu. Babu shakka kamfanonin ketare za su ci riba idan suka zuba jari da aiwatar da ayyukansu a kasar Sin.
Wang Wenbin ya bayyana cewa, kasar Sin ta samu kyakkyawan mafarin bunkasuwar tattalin arziki a bana, wanda ya zama abin misali a duniya a fannin raya tattalin arziki. Ya ce mahalarta da dama sun halarci taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa na samun bunkasuwa na kasar Sin, da kuma taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa na Asiya na Boao.
‘Yan kasuwa da dama sun nuna imani ga karfin tattalin arzikin Sin, da makomar bunkasuwar kasar Sin. Sun ce kasuwar kasar Sin tana da babbar daraja ga kamfanonin ketare, kuma za su ci gaba da zuba jari a kasar Sin. (Zainab Zhang)