Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna da takwaransa na Amurka Joe Biden a jiya Talata ta wayar tarho, bisa bukatar shugaba Biden. Shugabannin biyu sun yi tattaunawa mai zurfi da musayar ra’ayi kan dangantakar kasashensu da batutuwan da ke jan hankulansu.
Shugaba Xi ya bayyana cewa, ganawarsa da shugaba Biden a watan Nuwamban bara a birnin San Francisco, ya bude wata mahangar makomarsu. Ya ce cikin watannin da suka gabata, jami’an kasashen biyu sun aiwatar da matsayar da suka cimma sahihanci. Kuma dangantakar Sin da Amurka ta fara daidaituwa, sannan al’ummomin kasashen biyu da ma na kasa da kasa na maraba da hakan. Ya ce a daya bangaren, abubuwan dake yin mummunan tasiri kan dangantakarsu na karuwa, don haka akwai bukatar bangarorin biyu su mayar da hankali kan su.
- Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Fadada Yankunan Tudu Na Teku Da Take Iko Da Su
- Sin Ta Mai Da Martani Ga Yadda Amurka Ta Gyara Matakin Kayyade Fitar Da Kayayyakin Sassan Laturoni Zuwa Ketare
Shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, batun Taiwan shi ne iyaka ta farko da bai kamata a tsallake ba a dangantakar kasashen biyu. Ya ce kasar Sin ba za ta nade hannu tana kallon ayyukan ‘yan aware masu neman ‘yancin yankin da tallafi da goyon bayan da ake ba su daga waje ba.
A nasa bangaren, shugaba Biden ya ce dangatakar Sin da Amurka ita ce mafi tasiri a duniya. Kuma ci gaban dangantakar da aka samu bayan ganawarsu ta San Francisco, ya nuna cewa bangarorin biyu za su iya inganta hadin gwiwarsu tare da hakuri da bambance-bambancen dake akwai tsakaninsu.
Joe Biden ya kuma nanata cewa, Amurka ba ta neman tada sabon yakin cacar baka, kuma ba ta da muradin sauya tsarin kasar Sin, haka kuma kawancen da take yi ba ya nufin yi wa Sin taron dangi. Kazalika, Amurka ba ta goyon bayan ‘yancin yankin Taiwan, kuma ba ta neman tada rikici tsakaninta da Sin. Bugu da kari, ya ce Amurka tana goyon bayan manufar Sin daya tak a duniya.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya yi karin haske a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau, game da tattaunawa ta wayar tarho, tsakanin shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Amurka Joe Biden, kan batutuwan sashen tudun ruwa na Ren’aijiao, da yankin Hong Kong, da jihar Xinjiang, da ta Xizang da sauransu.
Game da batun sashen tudun ruwa na Ren’aijiao, Wang Wenbin ya bayyana cewa, a yayin tattaunawar, Sin ta jaddada cewa, tana da ikon mallakar tsibiran Nansha, da yankin teku dake dab da su, wadanda suka hada da tsibirai da sassan tudun ruwa, da yankunan rairayi, ciki har da sashen tudun ruwa na Ren’aijiao.
Wannan batu dai ya biyo bayan yadda bangaren kasar Philippines ya yi ta sabawa alkawarin da ya dauka, ta hanyar yunkurin kafa sashensa na dindindin a kan tsibirai, da sassan tudun ruwa na kasar Sin da babu mutune a kansu, da nufin sace ikon mallakar sashen tudun ruwan Ren’aijiao. Bangaren Sin na ganin Amurka ba ta da nasaba da wannan batu na yankin kudancin tekun kasar Sin, don haka bai kamata ta tsoma baki cikin batun Sin da Philippines ba.
Game da batun jihar Xinjiang da ta Xizang, Wang Wenbin ya jaddada cewa, batun Xinjiang da Xizang, batu ne na cikin gidan kasar Sin. Kaza lika kasar Sin na dora muhimmanci sosai kan kare hakkin dan Adam. Ya ce, jama’ar kasar ne ke da ikon bayyana ra’ayinsu kan kare hakkin dan Adam na kasarsu.
A daya bangaren, kasar Sin tana fatan yin mu’amala tare da Amurka, kan batun kare hakkin dan Adam bisa tushen girmama juna, sai dai Sin din ba za ta amince da duk wani nau’in aiki na tsoma baki cikin harkokin cikin gidanta bisa hujjar kare hakkin dan Adam ba. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha&Zainab Zhang)