• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Faidar Tattaunawar Baya-bayan Nan Ta Shugabannin Sin Da Amurka

by CGTN Hausa
2 years ago
Amurka

Masharhanta da dama na ci gaba da tofa albarkacin bakin su, game da tattaunawar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi ta wayar tarho da takwaransa na Amurka Joe Biden da yammacin ranar Talata, zantawar da ta shiga muhimmin tarihi a kokarin da kasashen biyu ke yi na aiwatar da matakan yaukaka dangantaka da fahimtar juna. Kafin tattaunawar ta baya bayan nan, shugaba Xi da Biden sun gana keke-da-keke a tsibirin Bali na Indonesia a shekarar 2022, sun kuma gana a birnin San Francisco na Amurka a watan Nuwamban bara, kana sun zanta sau 5 ta wayar tarho.

Wannan dai tattaunawa ita ce ta farko a tsakanin shugabannin biyu, tun bayan da suka yi ganawar ido da ido a watan Nuwamban bara a birnin San Francisco, kuma ko shakka babu ana sa ran zantawar ta wannan karo za ta taimaka, wajen ingiza cimma burin da duniya ke da shi game da cimma daidaiton dangantaka tsakanin kasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya.

  • Bloomberg: Damuwa Game Da Karfin Sin Wajen Samar Da Hajoji Ba Ta Da Tushe
  • Sin Ta Musanta Rahoton Amurka Game Da Harkokin Cinikayya

Daga tattaunawar shugaba Xi da mista Biden, muna iya fahimtar burin sassan biyu na fatan cimma wasu muhimman kudurori a bana, tare da burin kaucewa sake shiga wata sabuwar turka-turka tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Xi dai ya bayyana manyan kudurorin kasar Sin don gane da dangantakarta da Amurka a bana, yana mai fatan sassan biyu za su martaba matakan wanzar da zaman lafiya, da fifita daidaito, da goyon bayan matakan amincewa juna.

Ko shakka babu idan har kasashen biyu sun amince, tare da aiwatar da alkawuran da suka daukawa juna a ganawar San Francisco, da kuma tattaunawar baya bayan nan, hakan zai ingiza cimma nasarar alakar dake tsakanin Sin da Amurka.

LABARAI MASU NASABA

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Masu fashin baki na ganin idan har kasashen biyu za su kai ga nasarar kyautata alaka, to wajibi ne su sauke nauyin dake wuyan su, ta hanyar martaba juna, su yi cudanya cikin lumana, kana su rungumi hadin gwiwar cimma moriyar juna, kana su ci gaba da yaukaka alaka bisa daidaito.

Muna iya cewa faidar ganawar shugabannin biyu ta kara fito da burin kasar Sin na jaddadawa bangaren Amurka muhimmancin inganta dangantakarsu, da fatan Amurka za ta dakatar da yunkurin danne kamfanonin Sin, kana ta nuna sanin ya kamata don gane da batun zirin Taiwan da tekun kudancin Sin.

A daya bangaren, shugaba Biden ya sha alwashin cika alkawuran da Amurka ta dauka a baya, inda ya jaddada muhimmancin dangantakar Amurka da Sin, yana mai nanata cewa Amurka ba ta neman tada sabon yakin cacar baka, kuma ba ta da muradin sauya tsarin kasar Sin, haka kuma kawancen da take yi da sauran sassa ba ya nufin yi wa Sin taron dangi ko mayar da ita saniyar ware.

Muna iya cewa, idan har kalaman shugaba Biden suka dace da matakan zahiri da Amurka za ta dauka a nan gaba, ko shakka babu sassan biyu za su kai ga cimma nasarar bunkasa kan su, da kuma haifar da babbar faida ga bunkasar tattalin arzikin duniya baki daya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26
Daga Birnin Sin

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Next Post
Xi Ya Taya Sabuwar Shugabar Malta Murnar Kama Aiki

Xi Ya Taya Sabuwar Shugabar Malta Murnar Kama Aiki

LABARAI MASU NASABA

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

October 9, 2025
Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

October 9, 2025
SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025
An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.