Hukumar kula da jiragen kasan Nijeriya ta tara naira biliyan 1.07 a matsayin kudin shiga daga wajen fasinjoji a zango na hudu na shekarar 2023, a cewar rahoton hukumar kula da kididdiga ta kasa (NBS) a rahoton da ta fitar a ranar Litinin a Abuja.
Rahoton ya nuna cewa kudaden sun yi kasa ne ma da kaso 7.51 cikin dari idan aka kwantata da abun da hukumar ta tara na biliyan 1.15 a zango na hudu na shekarar 2022.
- Wani Dansanda Mai Rakiyar Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Abuja Ya Rasu Acikin Jirgin
- NRC Ta Dakatar Ma’aikacinta Kan Karbar Kudin Fasinja Ba Bisa Ka’ida Ba
Kudaden shiga da aka samu daga kayayyaki ya kama da kaso 169.16 na naira miliyan 423.22 daga miliyan 257.23 da aka samu a wannan wa’adin lokacin.
“An samu karin kaso 3.02 cikin dari a wannan fannin daga naira miliyan 382.17 da aka tara a karshen zangon 2022 zuwa naira miliyan 393.72 a zango na hudu na 2023,” rahoton ya ce.
A cewar rahoton, yawan adadin fasinjojin jiragen kasa ya ragu a zango na hudu na 2023 da kaso 49.73 zuwa 672,198 sabanin 1,337,108 a wa’adin da ya gabata.
Hukumar ta ce adadin fasinjojin jiragen ya ragu da kaso 32.08 daga 3,212,948 da aka samu a 2022 zuwa 2,182,388 a 2023.
NBS ta kara da cewa adadin kudin shiga da hukumar ta samar shi ma ya samu nakasu da kaso 2.64 a 2023, idan aka kwatanta naira biliyan 4.55 da hukumar ta amsa daga wajen fasinjoji a shekarar 2022 da ya zama biliyan 4.43 a 2023.
“Kazalika, yawan kudin kaya da kudaden da aka samu daga manyan jiran kasa suka kwaso ya karu a 2023 da kaso 102.04 da 144.32 sabanin na 2022,” a cewar rahoton.