Hukumar kula da harkokin ba da tabbacin kiwon lafiya ta kasar Sin ta bayyana a kwanan baya cewa, tsarin ba da tabbacin kiwon lafiyar kasar Sin ya ba da taimakon jinya kyauta ga mafiya rauni marasa lafiya miliyan 250 a shekarar 2023. Tsarin ba da taimakon jinya kyauta ga mafiya rauni, wani muhimmin bangare ne na tsarin ba da tabbacin kiwon lafiyar kasar Sin, wanda ke tabbatar da ba da hidimomin kiwon lafiya ga marasa galihu. An yi gwajinsa ne a yankunan karkara da biranen kasar Sin a shekarar 2003 da ta 2005, bi da bi.
A cewar hukumar, irin wadannan kudaden taimakon jinya ya karu daga kudin Sin RMB yuan biliyan 1.38, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 194.5 a shekarar 2005, zuwa yuan biliyan 74.5 a shekarar 2023.
A halin yanzu, a yawancin sassan kasar Sin, mafiya rauni ba sa bukatar biyan kudin magani mafi kankanta, kamar yadda suka yi a baya, don samun taimakon jinya. (Yahaya)