A karshen watan Fabrairun shekarar 2024, adadin tashoshin 5G na kasar Sin ya karu zuwa fiye da miliyan 3.5, kamar yadda sabbin alkaluma daga ma’aikatar masana’atu da fasahar sadarwa ta kasar Sin (MIIT) suka nuna.
Yayin da tashoshin 5G ke kara karuwa, ana kuma fadada amfani da fasahar 5G a masana’antu, tare da gaggauta hada fasahar zamani ta digital da kuma tattalin arziki na hadaka.
- Hukumar NPA Ta Samar Da Naira Biliyan 501 Ga Asusun Kasa A 2023 – Bello Koko
- Sojojin Sin Da Amurka Sun Gana A Hawaii Don Tattauna Batun Tsaron Teku Da Na Sararin Sama
Daga hakar ma’adinai ta hanyar amfani da fasahar zamani zuwa masana’antun zamani da kuma jigilar kaya ta hanyar zamani, ana amfani da fasahar dijital cikin sauri da inganci a sassa daban daban a kasar Sin. Alkaluman MIIT sun nuna cewa, ana amfani da fasahar 5G cikin manyan sassan tattalin arziki guda 71 a kasar Sin.
Zhao Zhiguo, babban injiniyan ma’aikatar MIIT, ya ce ma’aikatar za ta ci gaba da inganta sauye-sauyen masana’antu zuwa na dijital, da aiwatar da shirin AI Plus, wato amfani da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam a sana’o’i daban daban, don hanzarta habaka sabbin masana’antu da fasahar zamani ke karfafawa.
Za kuma a yi kokarin inganta yin amfani da fasahar ta 5G a sassa daban daban, don samun karin sabbin kirkire-kirkire da sakamako mai kyau, a cewar Zhao. (Yahaya)