Shafin yanar gizo na jaridar Lianhe Zaobao ta kasar Singapore, ya wallafa rahoton yanayin da kasashen kudu maso gabashin Asiya ke ciki na shekarar 2024, inda ya ce karo 6 a jere, ofishin nazarin ASEAN, na cibiyar binciken yankin kudu maso gabashin Asiya, ko ISEAS-Yusof Ishak, ta gabatar da wannan rahoto.
Rahoton ya fitar da bayanai game da matakan da kasashen wannan yanki ke dauka kan Amurka da Sin, da amincewarsu ga wadannan kasashe, kuma ya tattaro ra’ayinsu game da batutuwan da suka fi jawo hankalin mutanen wannan yanki.
- Ana Sa Ran Samun Tafiye-tafiyen Fasinjoji Fiye Da Miliyan 750 Yayin Hutun Bikin Qingming
- Ana Sa Ran Samun Tafiye-tafiyen Fasinjoji Fiye Da Miliyan 750 Yayin Hutun Bikin Qingming
Rahoton ya bayyana cewa, bincikin jin ra’ayin jama’a da aka gudanar ya nuna cewa, kasashen wannan yanki na ci gaba da kallon kasar Sin a matsayin kasa dake yin tasiri mai fa’ida a fannin tattalin arziki da siyasa a yankin. Kaza lika idan za a zabi kasar da suka fi so, yawancinsu za su zabi kasar Sin, inda a karon farko yawan masu zabar Sin ya zarce na Amurka, tun fara gudanar da nazarin a shekarar 2020.
A daya bangaren kuma, wadanda aka jin ra’ayinsu sun amince da makomar alakar kasashensu da Sin, inda kwarin gwiwarsu ya ragu don gane da amincewa da Amurka a matsayin abokiyar hadin kai, da kare tsaron yankin.
An ba da labarin cewa, mutane 1,994 sun gabatar da ra’ayoyinsu a binciken da aka gudanar, a bangarorin ilmi, da kimiyya da fasaha, da kasuwancin sassa da hukumomi masu zaman kansu, da kafofin yada labarai. Sauran sun hada da hukumomin kasa da kasa, da na shiyyoyi, wadanda suka gabatar da ra’ayoyin su ta intanet, daga ranar 3 ga watan Jarairu, zuwa 23 ga watan Fabrairun da ya shude. (Amina Xu)