Jami’an hukumar farin kaya na civil defense a Jihar Katsina, sun dakile yunkurin da ‘yan bindiga suka yi na kai hari kan rumbun ajiyar kayayyakin abinci na gwamnati da ke yankin karamar hukumar Datsinma.
Cikin sanarwar da ya fitar a yau Lahadi, kakakin rundunar Buhari Hamisu, ya ce ‘yan bindigar sun kai farmakin ne da misalin karfe 1 na daren ranar Asabar, da zummar fasa rumbun ajiyar abincin.
- Shagulgulan Karamar Sallah: Me Aka Shirya Da Zai Bambanta Bara Da Bana?
- Garkuwa Da Mutane: Yadda Dimbin Jama’a Suka Tarbi Wadume Bayan Shafe Shekaru A Gidan YariÂ
Kakakin ya ce sai dai dakarunsu suka shafe sama da sa’o’i biyu suna musayar wuta da maharan kafin daga bisani Allah ya ba su sa’ar fatattakarsu bayan jikkata da dama daga cikinsu.
Bayanai sun ce mahukunta na amfani da majiya ko katafaren rumbun hatsin da ‘yan ta’addan suka kai wa farmaki ne wajen rarraba wa wasu daga cikin mazauna jihohin Katsina da Sakkwato da kuma Zamfara tallafin abinci.
Harin na ranar Asabar ya zo ne kwana guda bayan da ‘yansandan jihar Katsina suka sanar da kashe wasu ‘yan bindiga biyar
Kazalika sun ceto mutane fiye da 100 da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da su, yayin da kuma suka kwato shanu 658 daga hannunsu.