Ya zuwa yanzu dai, Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa zagon kasa (EFCC) ta kwato wa Gwamnatin Tarayya Naira Biliyan 30, yayin da ta kuma sanya asusun ajiyar banki 50 a binciken da ake yi wa tsohuwar ministar harkokin jin kai da yaki da fatara, Betta Edu da wata ma’aikaciyar Ma’aikatar, Halima Shehu.
Kimanin watanni uku da suka gabata ne shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Betta Edu da Halima Shehu saboda zargin karkatar da makudan kudade.
- Kotu Ta Bai Wa EFCC Umarnin Ci Gaba Da Tsare Emefiele
- EFCC Za Ta Gurfanar Da Masu Motocin Da Aka Kama Da Kayan Abinci A Borno
Nan take kuma, Shugaban ya dakatar da shirin na Tallafi da rage talauci (NSIP), sannan ya bukaci hukumar EFCC da ta binciki jami’an da ke da hannu acikin badakalar.
Bayan watanni uku, shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, wanda ya bayyana haka, ya ce, hukumar na samun nasarorI a binciken.