A yau gidauniyar tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki ke kammala rabon abincin buda-baki da ta ke yi cikin azumin Ramadan.
An fara rabon abincin a ranar 15 ga watan Ramadan a jihohin Arewa guda biyar da suka hada da Sakkwato da Kogi da Neja jihar Kwara da kuma babban birnin tarayya, Abuja.
- HOTUNA: Yadda aka Gudanar Da Idin Karamar Sallah A Jere
- Sallah: Ganduje Ya Bukaci Musulmai Su Yi Wa Nijeriya Addu’a
Saraki, wanda tsohon gwamnan Jihar Kwara ne, kuma tsohon shugaban majalisar dattawa daga 2015 zuwa 2019, ya jima yana irin wannan hidima a kowane watan Ramadan a karkashin gidauniyarsa.
Dubban mutane ne ke amfana daga rabon abincin wanda ake yi a masallatai da gidajen gyaran hali da sauran wuraren da mabukata a yayin buda-baki.
Gidauniyar Abubakar Bukola Saraki, dai ta dade tana irin wannan aikin na taimaka wa mabuƙata a lokuta da dama kuma a wannan shekarar ma ta ɗauki nauyin ciyarwar kamar yadda ta saba.
Shirin na da nufin rage wa al’umma wahalhalun da suke sha musamman wajen samun abin da za su ci a yayin da al’ummar kasar nan ke ci gaba da shan wahala sakamakon tashin kayan abinci da ragowar kayan masarufi.