Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya gana da tsohon shugaban jam’iyyar Kuomintang ta kasar Sin Ma Ying-jeou a yau Laraba a nan birnin Beijing.
A wannan rana, kakakin ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na majalisar gudanawar kasar Sin Zhu Fenglian, ta yabawa Ma Ying-jeou, wanda ya jagoranci tawagar matasa daga yankin Taiwan na kasar Sin a ziyarar da tawagar ta kawo Beijing, a kan muhimmiyar gudummawar da ya bayar wajen inganta mu’amala tsakanin matasa a gabobi biyu na zirin Taiwan, wato babban yankin kasar Sin da yanki na Taiwan. (Mai fassara: Yahaya)