Akalla alhazan kasar Bangladesh 88 ne suka rasu a cikin watanni daya da rabi da suka gabata a zamansu a kasar Saudiyya a yayin gudanar da aikin hajjin bana da aka kammala.
Muhammad Maqsudur Rahman, Babban Shugaban Ofishin Haajjin Bangladesh a Saudi Arabiya, ya shaida wa manema labarai a yau Lahadi cewa kashi 90 cikin 100 na wadanda suka rasu sun haura shekaru 60, yayin da biyar zuwa shida daga cikinsu basu kai shekarun ba.
- Majalisar Zartaswa Ta Yi Wa Osinbajo Fatan Samun Sauki
- Kasar Sin Za Ta Inganta Manufofin Taimakawa Dukkan Bangarorin Tattalin Arziki
Daga cikin wadanda suka rasu 77 maza ne, mata kuma 11, in ji Maqsudur.
Mafi akasarin tsofaffin alhazan sun rasu ne sakamakon bugun zuciya da shanyewar barin jiki da kuma ciwon koda, yayin da biyu suka mutu a wani hatsarin mota, shi kuma wani Alhaji ya rasu sakamakon fadowa daga wani tsauni da ke guraren ibada a garin Makka, in ji shugaban.
Da aka tambaye shi, Maqsudur ya ce tsofaffin alhazai, a mafi yawan lokuta, sun mutu ne sakamakon zaunannun cututtuka daban-daban a jikinsu da kuma sauran matsalolin lafiya.
Ya ci gaba da cewa, likitocin Bangladesh suna bayar da ayyukan kiwon lafiya ba dare ba rana ga dukkan alhazan kasar, inda ya kara da cewa kuma suna da adadin magungunan da ake bukata.
Maqsudur ya ce, an yi jana’izar dukkan wadanda suka mutu a kasar Saudiyya kamar yadda ‘yan uwansu suka bukata.