Alhamdu lillah. Masu karatu muna muku barka da Sallah. Muna kauna daga Allah, ya karbi ibadunmu, ya ba mu zaman lafiya da ci gaba a kasarmu da duk kasashen musulmi har ma da duniya baki daya.
Idan ba a manta ba, kafin watan Ramadan ya kama, darasinmu a wannan shafin yana bayani ne a kan rantsuwar da Allah ya yi da uba da dan da ya haifa wanda Malamai suka fassara mana cewa, uban ana nufin Annabi Ibrahim (AS) dan da uban ya haifa kuma ana nufin Annabi (SAW). Duka dai nuni ne a kan rantsuwa da darajar Manzon Allah (SAW).
- Girman Darajar Manzon Allah S.A.W Da Allah Ya Yi Rantsuwa Da Ita (3)
- Allah Ya Yi Rantsuwa Da Girman Darajar Manzon Allah S.A.W (2)
Za mu ci gaba kamar haka: A wani wuri kuma, a cikin Alkur’an maigirma inda Allah ta’ala ya ce “Alif lam miym, zalikal kitaab…”, Sayyidina Abdullahi bin Abbas (RA) ya ce wadannan haruffan rantse-rantse ne da Allah ya yi da su. Ma’ana Allah ya rantse da Alif, ya rantse da Lam kuma ya rantse da Minjaye. Allah ya rantse da su sai ya ce a (aya ta gaba) “wannan littafin (Alkur’ani) babu kokwanto a cikinsa”.
Sahlu Abdullahis Tustari ya ce wannan rantsuwa ce, ma’anar Alif din nan tana nufin “farkon sunan Allah”, ita kuwa Lamin tana nufin “karshen sunan Mala’ika Jibrilu”, sannan Minjaye tana nufin “farkon sunan Muhammadu”. Malam Samarkandi ya ruwaito wannan fassarar. To, idan aka tafi a kan wannan fassarar ta Tustari da Samarkandi, ma’anar wannan rantsuwar daga Alifun ita ce wato kamar Allah ya ce ne “Ni ne Allah, na saukar da Jibrilu zuwa ga Muhammadu da wannan littafin da babu kokwanto a ciki”. Malamai sun ce ko a nan ya isa a ga girman Manzon Allah (SAW). Suka ce, Alif da aka rantse da shi farkon sunan Allah ne, Minjaye da aka rantse da ita farkon sunan Annabi ne ‘Muhammadu’ amma da yake ba a shiga tsakanin Allah da Manzon Allah’ sai shi Mala’ika Jibrilu aka dauko karshen sunansa, wato Lamin din nan. Da shi ma dauko farkon sunansa za a yi, abin sai ya zama Alif (na Allah), Jiymun (na Jibrilu) da Miymun (na Muhammadu SAW). Wannan ma manuniya ce a kan girman Manzon Allah a wurin Allah (SWT).
Sannan har ila yau, an sanya Jibrilu a tsakani ne don koya wa halitta baki daya yadda za su rika bin wasida ko tsani na neman abu. Misali, kar mutum ya ce zai nemi ilimi amma shi zai karantar da kansa da kansa, ba zai je wurin wani malami ba. Ko mutum zai yi sana’a amma ya ce da kansa zai yi ba tare da ya samu wani ubangida ya koya masa ba. Wannan fassarar Samarkandi ya ruwaito ta ce ta hanyarsa, bai ce daga Tustari ne ba. Wato kowa yana da hanyarsa daban.
A wata fuskar kuma, wadannan haruffan Allah ya rantse da su ne cewa wannan littafin gaskiya ne babu kokwanto a cikinsa. Har ila yau, hada sunan Allah da na Manzon Allah a cikin haruffan yana nuna matsayi da girman Manzon Allah (SAW).
Malam Ibn Ada’u ya ce, ayar ‘Kaaf’ (Suratu Kaaf) rantsuwa ce da Allah ya yi da karfin zuciyar masoyinsa (SAW). Zuciyar Manzon Allah tana da karfi sosai fiye da yadda ake iya tunani. Domin Alkur’ani da Allah ya saukar a zuciyar Manzon Allah ya saukar kuma ta iya daukawa, da za a saukar wa dutse zai ragargaje. Amma kuma sai ga shi; shi (Manzon Allah) an saukar masa a zuciyarsa kuma ya iya daukawa.
Zuciyar Manzon Allah (SAW) ita ce babbar na’urar da ta iya daukar Alkur’ani saboda nauyinsa (kaulan thakiylan) har sauran al’umma suka samu sauki suna iya daukawa.
Haka nan, zuciyarsa (SAW) ta iya daukar ganin Allah. Shi Annabi Musa (AS) da aka yi masa tajalli sai da ya fadi ya suma. Amma Annabi (SAW) bai suma ba, ba ma kawai bai yi haka ba kadai; hatta al’ummarsa ma bai manta da su ba. Gafara da rahamar da ya roka wa al’ummarsa (a cikin Bakara) duk a gaban Zatin Allah aka yi su. Wannan ya isa ya nuna karfin Annabi. Shi Annabi Musa (AS) ma Malamai sun ce Zatin Allah da ya yi Tajalli ko girman kan allura bai gani ba.
Watakila kuma aka ce wannan harafi na “Kaaf”, sunan Kur’ani ne, ma’ana Kur’anu, wannan Kahuwau din farkon sunan Kur’ani ne, to kuma Allah ya yi rantsuwa da Kur’ani ne a gaba kuma ya kara kawo rantsuwar da sunan Kur’ani kuru-kuru? To, Malamai dai sun fadi haka. Watakila kuma aka ce “Kaaf” sunan Allah ne. Kila kuma “Kaaf” wani dutse ne da ya kewaya duniya ana ce ma sa “Jabalu Kaaf”. Akwai duntsen da ya kewaya duniya, sannan kuma duwatsun kankara suka kewaya. Wannan dutsen da shi Allah ya yi wa duniya Katanga don kar ta kife ko ta yi yawo da mu. Su kuma duwatsun kankara Allah ya kewaya duniya da su don kar rana ta kona mu. Haka kuma an ce fassarar “Kaaf” wanin wannan ne.
Sayyidina Ja’afara bin Muhammadus Sadik (Sharifi dan Manzon Allah SAW) ya ce, ana fassara rantse-rantsen da Allah ya yi a Alkur’ani da Manzon Allah ne. In ma dai Allah ya rantse da Zuciyar Manzon Allah ko kuma da Manzon Allah dukansa (SAW). Sayyidina Ja’afarus Sadik ya fassara rantsuwar da Allah ya yi da “Wannajmi” a matsayin Manzon Allah. Ma’anar “Wannajmi” a zahiri, Allah ya yi rantsuwa ne da Tauraron Surayya idan ya fadi. Amma a wurin Ja’afarus Sadik, ana nufin Annabi Muhammadu ne (SAW). Ya ce, wannan tauraron Zuciyar Annabi Muhammadu ne. Zuciyar Manzon Allah abu ne mai girma, sirri ne mai girma a wannan wurin. Don haka ya ce rantsuwar da Allah ya yi da “Wannajmi”, ya yi ne da Manzon Allah. Fassarar “izhaa hawaa” kuma ba yana nufin idan tauraro ya fadi ba ne, yana nufin yalwar Zuciyar Manzon Allah ne. Ya kuma ce, a wata fassarar, Allah ya rantse da zuciyar Manzon Allah ne don ta yanke ga barin komai sai Allah. Manzon Allah babu kowa a gabansa sai Zatin Allah. A koyaushe yana cikin Zikirin Allah. Makka gari ne na Aljannu, in kana duba tarihin Makka za ka ga haka. A nan ne Jinnun Nasibiyn suka zo suka ba da gaskiya da shi. Wurin da kowa yake tsoron zuwa amma shi Manzon Allah haka zai rika shiga cikin dare, cikin duwatsu da kogo yana ta Zikiransa. Da akwai tsoron wani ba Allah ba, zai iya firgita shi.
Alkur’ani ya zo da rantse-rantse da yawa. Akwai rantsuwa ta harafi, kamar “Alif-lam-miym”, akwai rantsuwa ta kalma, kamar ya ce “Wannajmi izhaa hawaa” ko ya ce “Wasshamsi wa duhaahaa”. Wadannan rantse-rantse ilimi ne mai yawa. Kuma an ce asirai ne na Allah Tabaraka wa Ta’ala.
Shehu Ibrahim Inyass (RTA) a cikin Tafsirinsa na ayar “Kaaf…”, yake cewa akwai halaye guda uku da muke da su. Akwai halin zuciya na Dan Adam, akwai halin aiki na Dan Adam, akwai halin harshe na Dan Adam. Haka Musulunci ma yake, Musulunci kudircewa ne a zuciya, fada ne da baki, aiki ne da jiki. Ka kudirce babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ka fadi La’ilaha illallah da baki, sannan a ga kana aiki da jiki wurin yin Sallah da Azumi da sauransu. To, a duk cikin wadannan halayen guda uku, akwai wani hali da ba mu san shi ba sai dai bin Allah kawai. Misali, a cikin halin aiki, ba mu san mece ce ma’anar mu je mu debi duwatsu muna jifa da su a wani waje da sunan muna jifan shaidan ba. Domin mu ba shaidan din muka gani ba, ba shaidan din kuru-kuru a wajen amma kuma tun da Shari’a ta yarda a yi, Manzon Allah (SAW) ya fada mana shikenan sai aikatawa kawai. Ko mun iya ganewa, ko ba mu iya ganewa ba dole mu yi. Haka idan aka dubi ibadar Safa da Marwa, tafiya ake yi a tsakanin wani dutse zuwa wani, amma tun da Shari’a ce ta ce a yi, sai a yi kawai ko mun gane; ko ba mu gane ba. Haka nan Arfa, zama za mu yi a wurin, an yarda mu yi Sallar Azuhur da La’asar a nan, amma ba a yarda mu yi Magriba da Isha’i a nan ba don ma kar mu zaci Sallah ta zaunar da mu a nan sai mun kai Muzdalifa. A can kuma zama kawai ake so mu yi. Ka ga duk wadannan sai dai bi kawai, babu tilas sai mun gane kafin mu yi. Ma’anar irin wadannan ibadun ba kowane Musulmi ne ya sani ba, amma kuma suna kan kowane Musulmi ya aikata da ya samu damar zuwa Hajji. Tun da Allah ne ya ce a yi shikenan sai aikatawa kawai, walau ka gane ko ba ka gane ba. Wannan hali na aikinmu kenan.
Haka nan a cikin kudircewarmu, Manzon Allah ya ba mu labari cewa mu yi imani da Allah kuma sako ne daga Allah. Mun yi imani ba tare da cewa dole sai mun ga Allah ba.