A ranar 11 ga watan Afrilu, aka fara gudanar da wani horo na musamman kan gina “koren babbar ganuwa” a kasashen Afirka, a nan birnin Beijing. Jami’ai 30 daga kasashe 9 da kungiyoyin kasa da kasa da suka hada da Najeriya, Habasha, Masar, Saliyo, Namibiya, da kungiyar Tarayyar Afirka sun halarci wannan horon.
Wannan horon zai dauki tsawon kwanaki 14, kuma zai gudanar da ayyuka kamar koyarwa a cikin ajujuwa, ziyarce-ziyarce, da musayar ra’ayi don musayar gogewa kan rigakafin kwararowar hamada. (Mai fassara: Yahaya)