Cinikayyar shige da fice ta Sin ta bunkasa da kaso 5 bisa dari, a rubu’in farko na shekarar nan ta 2024, idan an kwatanta na makamancin lokacin shekarar bara, kamar dai yadda alkaluman da hukumar kwastam ta kasar ta fitar a Juma’ar nan suka tabbatar.
Daga watan Janairu zuwa Maris, cinikin waje na kayyayakin kasar Sin ya kai yuan tiriliyan 10.17 kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 1.43, a cewar hukumar kwastam ta kasar. (Mai fassara: Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp