A ranar Asabar ne Hukumar Kwastam reshen tashar jiragen ruwa na Apapa ta sanar da samun nasarar tattara fiye da naira biliyan 489.6 a mastayin haraji a tsakanin 1 ga watan Janairu zua ranar 31 ga watan Maris 2024.
Bayanin haka yana cikin takardar manema labarai da jami’n watsa labarai na hukumar, Usman Abubakar, ya sanya wa hannu, ya ce kudin shigan da aka tattara a zangon farko na shekarar 2024 ya fi abin da aka tattara a shekara 2023 da kashi 100.
- Liu Yuxi Ya Halarci Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kan Sin Da Afirka Karo Na Uku
- Yawan Motocin Da Sin Ta Sayar Ya Kai Miliyan 6.72 A Rubu’in Farkon Bana
Sanarwar ta kuma jinjina ga jami’an kwastam na yankin a kan jajircewarsu da kuma goyon bayan da suke ba shugaban kwastam na yankin, Comptroller Babajide Jaiyeoba, sun kuma nemi a ci gaba da bayar da irin wannan goyon bayan don tabbatar da ci gaban da ya kamata a nan gaba.
Jami’in watsa labaran ya kuma tunatar da jami’an kwastam a kan cewa, reshen hukumar na Apapa na da muhimmin rawar takawa a kokaruin cimma kudadden da hukumar take hankoron tarawa a wannan shekarar wanda ya kai naira tiriliyan 5.7. a kan haka dole kowa ya bayar da nasa gudummawar.
Ya ce, za a iya tattara wadannan kudaden a cikin sauki in dukkan jamai’an suka mayar da hankali wajen gudanar da aikinsu a cikin gaskiya da rikon amana tare da kuma bin dokokin aikin.