Majalisar Wakilai ta bayyana dalilan da suka sa ta wanke Shugaban Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya NPA, Alhaji Mohammed Bello Koko daga zarge-zargen badaqalar bashin naira biliyan 178 da ke tattare a rahoton yadda hukumar ta gudanar da ayyukanta na shekarar 2019.
Shugaban kwamitin majalisar wakilai da ke sauraron korafe-korafe, Hon Mike Etaba, ya bayyana mastayar majalisar a zaman bayyanar jama’a da aka yi aAbuja a makon da ya gabata.
- Sin Na Goyon Bayan Yunkurin IAEA Na Tabbatar Da Tsaron Tashar Nukiliya Ta Zaporizhzhia
- Ana Gudanar Da Horo Kan Gina “Koren Babbar Ganuwa” A Afirka A Beijing
Idan za a iya tunawa wata kungiya mai zaman kantamai suna ‘Forum of Nongovernmental Organisations in Nigeria’ ta zargi NPA da Bello-Koko a kan badakalar naira biliyan 178 na kudaden da suka makale daga basukan da hukumar take bi wadanda ke tatteare a cikin rahotonin hukumar na shekarar 2019.
A yayin da aka ci gaba da zaman sauraron matsalar na bayyanar jama’a, kungiyar ba ta bayyana ba don ta kare zarge-zargen da ta ke yi a kan haka kwamitin ya yi watsi da zarge-zargen gaba daya.
Shugaban kwamitin Hon. Eytaba ya nuna takaicinsa a kan rashin bayyanar wadanda suka yi zargin don su kare tare da gabatar da hujjojin da ya kamata a kan haka ya yi watsi da zargin da suke yi wa NPA da shugabanta, Alhaji Mohammed Bello Kpko.
Ya kuma kara da cewa, “Wannan ne karo na shida da kwamitin ke zama amma wanda yake zargin bai gabatar da kansa a kan abin da yuake zargin NPA da shugabanta ba saboda haka mun yi watsi da zargin gaba daya.”