Wani Shugaban Gidauniyar Kasuwanci ta ChopLocal Katie Olthoff ya bayyana cewa, mafi akasarin mutane ba su damu da yin la’akari da lokacin da ya kamata su tsaya su kafa kawunansu tare da kuma kasuwancinsu ba.
A nan, ga matakai uku na samun nasarar sayar da Nama kai tsaye ga masu saye.
- Bikin Sallah: Ministan Yaɗa Labarai Ya Nemi ‘Yan Nijeriya Su Dawo Da Kyawawan Dabi’un Da Suka Jingine
- Shigar Da Japan Cikin AUKUS Kara Kuskure Manufar Kungiyar Ce
1- Kirkirar Dabarar Yin Kasuwanci:
Wannan hanya ta kirkirar dabarar yin kasuwanci, za ta yi matukar ba ka damar sanin inda za ka tunkura da kuma manufar da kake son cimma.
Kazalika, wannan dabara za ta kai ka ga janyo hankalin abokan cinikayya da kuma kara darajar ingancin sana’arka, ba tare da bata wani lokaci ba.
Haka nan, shi ma Matt LeRoud da ke a Jami’ar Cornell ya sanar cewa, kasuwanci hanya ce da ke sanya wa dan kasuwa fahimtar abubuwan da abokanan cinikayyasa ke bukata.
LeRoud ya ci gaba da cewa, ya kamata a fayyace dabarun kasuwanci tare da samar da manufar da kake son cimma a kasuwancinka, ciki har da la’akari da abokan cinikayyarka. A nan, manufar da kake son cimma; ba wai lallai sai don ka sayar da kayan ba ne, maiyiwuwa yadda za ka iya tuntubar akokan cinikayyarka ko kuma yin cinkiyayya da su ta hanyar kafar sada zamunta.
2- Bunkasa Hajarka:
Don samun cin nasara a kan hajar da kake son sayarwa, wajibi ne ka tabbatar ka samar da kayan da abokan cinikayyarka ke bukata.
Ka tabbata kana da masaniya a kan kasuwar cikin gida, sannan kuma ka rika bibiyar sauran kasuwannin da ke kan yanar gizo, don ganin irin kayan da suka baje na sayarwa da kuma yin dubi kan wadanne kaya ne suka fi karbuwa a kafar ta yanar gizon.
3- Daukar Shawarar Kwararru:
Ka tabbata kana daukar shawarar kwararru tare da sauraron abin da abokan cinikayar taka ke bukata.