Yadda za a nuna godiya har ila yau ga Malaman da suka fi yin kwazo amma akawai bukatar da bin hanyar da tafi dacewa wajen yi masu karin girma ba ma kamar wajen kawo ci gaban makarantar idon al’umma.
Irin wannan kyauta wajen karin girma wajen nuna cewar ana godiya a kan irin ayyukan da Malaman suke yi domin kara masu kwarin gwiwa, abin ba zai tsaya kan su kadai ba ne har ma ga wasu domin su ma su kara zage damtse wajen aikinsu.
- Ana Gudanar Da Horo Kan Gina “Koren Babbar Ganuwa” A Afirka A Beijing
- Bikin Sallah: Ministan Yaɗa Labarai Ya Nemi ‘Yan Nijeriya Su Dawo Da Kyawawan Dabi’un Da Suka Jingine
Alal misali ana ba Malamai su san irin ci gaban da suka samu wajen aikinsu na koyarwa daidai lokacin da ya dace, irin hakan na sa su kara maida hankali wajen da akwai bukatar yin hakan ga kuma bada kwarin gwiwa lamarin da zai ci gaba ne.
- Mu’amala ta gaskiya da Malamai
Mu’amala ta gaskiya tsakanin wanda ya mallaki makaranta da Malamai ita wata hanya ce ta ba su Malamai ta kara masu kwarin gwiwa, musamman ma Malamai da suke koyarwa a ta bangaren ilimin fasaha.A bayyane za su gane irin abin da za su iya samu a gaba, bada dama ta sanin halin da ake ciki da ya hada abubuwan da ake bukatar su koyar,ga kuma yin abubuwa baro- baro babu wata kunbiya- kunbiya wajen samun bunkasa ko kara kwarewar ci gaban aikin koyarwa.
Sa Malamai su bada tasu gudunmawar wajen daukar mataki yin hakan na san su ji har cikin zuciyarsu, su ma ba a manta da su ba an san ayyukan da suke yi, har sai an gano maganin matsalar da aka samu.
Wajen ban ikan irin ci gaban da Malamai suke samu na koyawa dalibai da irin yadda suke gane ko fahimtar abubuwan da ke koya masuyin haka yana matukar taimakawa da bada kwarin gwiwa na bangaren ilimin fasaha,ko shakka babu hakan na kara sa Malamai su gane cewar ana fahimtar abubuwan da suke koyawa ta amfani da fasaha.
Alal misali,ClassDojo,wata kafar ilimin da ta maida hankalinta kan wata kafa ta sadarwa da Malamai na matukar nuna yadda sanin halin da ake ciki na hakika.Sanin halin da Kamfani ke ciki lokaci zuwa lokaci wajen taro na tabbatar da ma’aikatan sun san irin muradan da Kamfani yake son cimmawa,ci gaba da kuma matsaloli.
Bayani mai gamsarwa na yadda ko wane ma’aikaci yake bada gudunmawa kan tafiya yadda sa ran cimma Muradin Kamfanin wajen nuna kowa yana da muhimmanci ta hanyar bda ta shi gudunmawa,a gudu tare a tsira tare.Yin abu ba rufa- rufa yana sa ma’aikata su gane irin gudunmawar da suke badawada amfaninta, su sa su fahimtar cewar suna da muhimmanci.
Ko dai za a iya samun mutum ta kafar sadarwa ta zamani idan kana da data, in dai makaranta ce da ake koyarwa, irin taimakon da kake badawa, ta ayyukan ofis,sayar da kayan kamfani, ko kai masanin Komfuta ne, kowa da akwai gudunmawar da yake badawa wajen bunkasa harkar koyarwa, ta hanyar kawar da duk wadansu abubuwan da za su iy kawo matsala wajen koyarwa a samu ilimi mai nagarta.
Bayan gudunmawar da suke badawa wajen lamarin da ya shafi ilimi maida hankalin wadannan masana harkar ilimi yawancin lamarin nasu yana tafiya hakanan ne ba godi bare nagode,bama kamar yadda albashinsu bai taka kara ya karya ba.Tsayawar da suke yi kai da fata saboda aikinsu na koyarwa abin wani babban mataki ne a harkar aikinsu ta yau da kullun.
Irin halin dattakon da suka nuna lokacin annobar cutar Korona abin a yaba ne bama kamar lamarin koyarwa daya shiga wani mawuyacin hali, idan har za a kalli taimakon da suka bada karami da babba ga masu koyo ya zama dole ne a gode masu.
Domin ci gaba da aiwatar da lamarin da yake mai taimakawa ne na sanin halin da ma’aikaci yake ciki ko abin da ya shafi aikin sa ko shi ma kan shi wata hanya ce ta kara dankon zumunci, da kuma nuna jin dadin abin da ma’aikanta su ke yi wajen tafiyar da Kamfaninka, ko da su Malaman makaranta ne ko akasin haka abu ne da zai matukar taimakawa wajen tafiyar ci gaban wurin.