Assalamu alaikum masu karatu barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Ado Da Kwalliya. Da fatan kun yi Sallah lafiya.
A yau shafin na mu zai zo muku da yadda za ku magance sanyi na mata da maza.
- Sin Ta Bayyana Rashin Jin Dadi Kan Binciken Da Eu Ta Yiwa Wasu Kamfanonin Sin Masu Samar Da Wasu Hajoji
- Sin Ta Yi Nasarar Gwajin Sadarwa Da Tauraron Dan Adam Na Queqiao-2 Na Binciken Duniyar Wata
Sanyi mai sanya kaikayi ko kuraje ko fitar ruwa ko rashin sha’awa da jin zafin jima’i ko rashi kuzari ga maza da dai sauran matsaloli. Kun san ita cutar ciwon sanyi aba ce mai matukar wahalar magani. Idan ke kin yi magani amma maigida bai yi ba to sanyi dai yana nan amma idan kun yi maganin ku biyu in sha Allahu za’a dace abu ne mai wahalar magani, idan kina da abokiyar zama har ita ya kamata ku yi maganin Allah ya sa mudace.
Abubuwan da za ku tanada:
Danyar Citta, Farar Albasa, Kanunfari, Tafarnuwa, Zuma.
Yadda za ku hada:
Idan kika samo kayan da muka ambata sai ki hada su waje daya ki zuba ruwa kamar lita daya 1, ki tafasa sannan ki sa zuma. Ki samu jarka ki juye a ciki, kullum ku rika shan kofi daya da safe, daya da yamma.
Kuma dole ma’aurata su sha maganin tare saboda ku samu sauki tare idan kuma aka yi maganin kala-kala babu sauki to anemi maganin jinnul.