Da yammacin yau Jumma’a, shugaban hukumar yada labarai ta ma’aikatar tsaron kasar Sin kuma kakakin ma’aikatar tsaron kasar, babban kanar Wu Qian, ya fitar da sako game da abubuwan da suka shafi aikin soja a baya bayan nan.
Game da batun Amurka na shirya girke makamai masu linzami masu tafiyar matsakaicin zango a yankin Asiya da tekun Pasifik a kwanan nan, Wu Qian ya bayyana cewa, abu ne mai hadari da Amurka ta inganta girke makamai masu linzami a yankin, wanda zai kawo barazana ga tsaron kasashen dake yankin, da kuma lalata zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, bangaren Sin na adawa sosai da hakan, kuma zai dauki matakai don magance shi.
Game da ziyarar kwamandan sojojin teku na yankin Taiwan a hedkwatar sojojin Amurka dake yankin Indo-Pasifik a Hawaii, Wu Qian ya ce, yankin Taiwan wani bangare ne na kasar Sin da ba za a iya raba shi daga kasar ba, warware batun yankin Taiwan harkar cikin gida ce ta Sin, ba a yarda da tsoma baki daga waje ba. Kuma rundunar sojin kasar Sin za ta dakatar da duk ayyukan dake yunkurin raba yankin Taiwan daga kasar Sin.(Safiyah Ma)