Shugabannin kasashen Amurka, Japan da Philippines sun gudanar da taron kolin bangarorin uku karo na farko a birnin Washington a ranar 11 ga wannan wata bisa agogon wurin. Bayan taron, bangarorin uku sun fitar da hadaddiyar sanarwa, inda suka zargin Sin cewa, ta “sauya halin da ake ciki yanzu ta hanyar karfin tuwo ta kashin kanta”, kuma sun nuna “damuwarsu” ga ayyukan kiyaye ikon mallakar kasa da Sin ta gudanar a yankunan tekun kudancin kasar da tekun gabashin kasar da dai sauransu.
Bisa rahoton da kamfanin dillancin labarai na AP na Amurka ya ruwaito, a gun taron tattaunawa na bangarorin ukun, Amurka ya nanata wa Philippines cewa, idan aka kai wa jiragen sama ko jiragen ruwa ko rundunar sojin Philippines hare-hare a yankin tekun kudancin kasar Sin, za ta iya samu tallafi bisa yarjejeniyar kare kai da Amurka da Philippines suka kulla.
Bangaren Sin a ko da yaushe yana nacewa kan manufar warware rikicin ikon mallakar kasa cikin kwanciyar hankali ta hanyar tattaunawa, amma ba ya nufin Sin za ta jure miyagun ayyukan da wasu kasashe suke aikatawa. A halin yanzu, Sin ta karfafa dangantakarta da kasashen kungiyar ASEAN, amma “karamin rukuni” na Amurka da Japan da Philippines ya yi akasin haka, wanda zai kawo yaki da barazana ga yankin. (Safiyah Ma)