Isra’ila ta rufe dukkanin makarantun a fadin kasar, a yayin da Iran ta kaddamar da hare-haren ramuwar gayya.
Kasar Isra’ila ta rufe makarantu a fadin kasar saboda fargaba, kamar yadda kakakin rundunar sojin kasar Daniel Hagari ya bayyana, bayan Iran ta mayar da martani kan wani mummunan harin da aka kai ofishin jakadancinta na Damascus.
Kasar ta ce ta dakatar da harkokin karatu a daidai lokacin da yanayin tsaro a kasar ke cikin tsaka mai wuya, a wata sanarwa da kakakin ya fitar ta kafar talabijin ta kasar.
Iran dai ta lashi takobin mayar da martani bayan harin da ake kyautata zaton Isra’ila ta kai a ranar 1 ga watan Afrilu wanda aka yi a ofishin jakadancinta a Damascus, inda ya kashe jami’an kare juyin-juya hali bakwai ciki har da janar-janar guda biyu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp