A ’yan kwanakin nan, an shiga zullumi a duniya dangane da yanayin da ake ciki da kuma abun da gaba za ta haifar game da rikicin Isra’ila da Falasdinu da a yanzu ya shafi kasar Iran. Kuma dangane da hakan ne, a jiya aka tattauna ta wayar tarho tsakanin ministan harkokin wajen Sin Wang Yi da takwarorinsa na Iran da Saudiyya.
Mun riga mun san cewa, kasar Sin ta samarwa kanta martaba da mutunci a idon duniya ta hanyar huldar mutunta juna da kuma cimma moriyar juna da kaucewa katsalandan da take aiwatarwa tsakaninta da kasa da kasa. Haka kuma, ko da yaushe, ta kasance mai kira da zaman lafiya da tattaunawa, maimakon nuna bangaranci ko ingiza rikici.
- Sin Na Cikin Kasashe Mafiya Tsaro A Duniya
- Gwamnatin Tarayya Na Biyan Tallafin Man Fetur A Asirce – El-Rufai
Tun bayan barkewar wannan rikici, kasar Sin ta yi ta kada kuri’ar goyon bayan kudurorin Kwamitin Sulhu domin tsagaita bude wuta ba tare da sharadi ba, tare da tuntubar bangarori masu ruwa da tsaki da zummar shawo kan rikicin.
Matsayin kasar Sin da kimarta ka iya taka rawa wajen ganin tankiyar dake tsakanin Isra’ila da Iran bai ta’azzara ba. Kamar yadda Wang Yi ya fada a tattaunawarsa da takwaransa na Iran Hossein Amir-Abdollahian, hari kan ofishin jakadancin Iran a Damascus, take dokokin kasa da kasa ne, amma kuma Iran za ta iya tafiyar da lamarin yadda ya kamata, tare da kiyaye zaman lafiya a yankin. Idan muka duba wannan matsayin na Sin, za mu gane cewa, sanin ya kamata irin nata bai sa ta rura wutar rikicin ko zuga Iran ta ci gaba da kai hare-hare ko ingiza yaki ba. Maimakon haka, ta nuna wa Iran cewa za ta iya shawo kan matsalar ba tare da ta’azzara yanayin da yankin ke ciki ba. Wannan shi ne abun da ya kamata kasa da kasa su yi, musamam masu karfin fada a ji.
Baya ga haka, a tattaunawar Wang Yi da takwaransa na Saudiyya Faisal bin Farhan Al Saud, Saudiyya ta ce tana sa ran ganin Sin ta taka rawa wajen samun zaman lafiya a yankin, kuma a shirye take ta hada hannu da Sin wajen cimma hakan. Saudiyya muhimmiya ce a yankin Gabas ta Tsakiya kuma neman goyon bayan Sin da ta yi, ya nuna cewa, ta aminta da Sin din, haka kuma ta yarda da yunkuri da shawarwarinta game da batun da ma rawar da take takawa a harkokin da suka shafi kasa da kasa a duniya.
A kullum, na kan bada misali da yanayin yawan al’umma da mabanbantan kabilu da ma mabiya addinai da Sin take da su da kuma zaman lafiya da ci gaban da suke morewa a kasar a matsayin abun koyi a duniya. Wadannan abubuwa da na zayyana, sun nuna karfi da gogewar Sin a harkokin da suka shafi tabbatar da zaman lafiya ba tare da zubar da jini ko tashin hankali ba. Haka kuma sun nuna cewa za ta iya taka rawa wajen tabbatar da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.