Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu, ya ce gwamnatin tarayya a baya-bayan nan ta kubutar da mutane sama 1000 daga hannun ‘yan ta’adda ba tare da biyan kudin fansa ba.
Ribadu, ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi malamai da dalibai 22 na Jami’ar Gusau da ke Jihar Zamfara, da aka kubutar da su daga hannun ‘yan bindiga a ranar Lahadi.
- Mun Damu Da Matsalar Yara ‘Yan Shila A Adamawa – Fintiri
- Da ÆŠumi-É—uminsa: Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kano Ta Sake Gurfanar Da Ganduje A Gaban Kotu
Idan ba a manta ba tun a ranar 22 ga watan Satumbar 2023 ne, ‘Yan bindiga suka shiga Jami’ar tare da yin awon gaba da sama dalibai da malamai 30.
A nasa jawabin shi ma da ya kasance a Jami’ar yayin karbar dalibai da malaman, mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mani Mummuni, ya jajanta wa iyalai da kuma hukumar makarantar bisa abin da ya faru.
Mataimakin gwamnan ya kuma bukaci hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen kubutar da sauran daliban da aka sace a wasu makarantun kasar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar, Yazid Abubakar ya fitar, ya bayar da tabbacin cewa rundunar za ta ci gaba da kokari wajen ganin an kubutar da sauran daliban da ke hannun ‘yan bindiga.