Kakakin ma’ikatar harkokin wajen Sin Lin Jian, ya bayyana a yau Laraba cewa, sigogin tattalin arzikin kasar Sin da suka hada da tubali mai kwari da juriya mai karfi da tarin fifiko da kuzari mai yawa da kuma dimbin damarmaki, ba su sauya ba.
Hukumar kula da kididdiga ta kasar Sin ta fitar da bayanai game da yanayin tattalin arzikin kasar a rubu’in farko na bana, wadanda suka nuna cewa tattalin arzikin kasar na ci gaba da farfadowa kuma ya fara da kyakkyawan mafari. Sai dai, wasu kafafen yada labarai na yammacin duniya sun fi mayar da hankali kan wasu alkaluma marasa kuzari, inda suke shakku game da ko Sin za ta iya cimma burinta na samun habakar tattalin arzikin da kaso 5 a bana.
- Idan Isra’ila Ta Kai Wa Iran Hari Ba Za Mu Goya Mata Baya Ba – Amurka
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Mata Da Yara, Sun Kashe Mai Unguwa A Wani Sabon Hari A Katsina
Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Lin Jian ya bayyana cewa, bayanan da hukumar kula da kididdiga ta kasar ta fitar sun bayyana cewa, alkaluma da dama sun nuna cewa tattalin arzikin kasar na ci gaba da farfadowa, kuma ya samu kyakkyawan mafari a bana. A baya bayan nan, ana kara jin muryoyin daga kasa da kasa, wadanda ke bayyana kwarin gwiwarsu game da kasar Sin, da kuma tabbacin da suke da shi kan ci gaban kasar.
Da yake mayar da martani ga wasu kasashen yamma dake bayyana damuwa game da karfin masana’antun Sin na samar da kayayyaki fiye da kima, Lin Jian ya nanata cewa, ikirarin cewa wai samar da kayayyaki fiye da kima da kasar Sin ke yi na mummunan tasiri ga kasuwar duniya, ba shi da tushe, ya kamata batun ya dogara da ka’idojin tattalin arzikin kasuwa.
Kakakin ya kuma yi gargadin cewa, daukar matakan kariyar cinikayya, zai kawo tsaiko ga yanayi mai karko na sarrafawa da samar da kayayyaki, lamarin da zai lahanta kokarin raya tattalin arzikin duniya ba tare da gurbata muhalli ba da kuma ci gaban masana’antu masu tasowa.
Ya kara da cewa, masana’antun sabon makamashi na kasar Sin sun samu fifiko ne daga sahihiyar basira da isasshiyar takara a kasuwa, maimaikon rangwame daga gwamnati. (Fa’iza Mustapha)