Shugabar kungiyar Bayar Da Tallafi Ga Marasa karfi da Farfado da Ruhin NIjeriya wato (Grassroots Mobilizers for Better Nigeria Initiative) Amb. Dr. Fatima Muhammad Goni, ta kai ziyara gami da kaddamar da raba kayan tallafi a Garin Dutse dake Jihar Jigawa.
Mai Martaba Sarkin Dutse Alhaji Muhammad Hamim Nuhu Sanusi CFR, shi ya karbi bakuncinta a Fadarsa da ke Garu, inda ya nuna farin cikinsa gami da yabo a gare ta da bayyana cewa masarautar da gwamnatin jihar suna sane da irin ayyuka da take gabatarwa.
- Gwamnatin Tarayya Na Biyan Tallafin Man Fetur A Asirce – El-Rufai
- Zulum Ya Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.3 Don Tallafawa Dalibai 997 Na Aikin Kiwon Lafiya
Makasudin wannan ziyara dai shi ne neman tabarruki da kuma nuna wa Mai Martaba Sarki wasu aikace-aikace da take yi na tallafa wa masu karamin karfi wajen ganin an gudu tare an tsira tare. Inda ta taba wasu muhimman banraori da suka shafi hidimta wa addini lafiya, da sauran fannoni da ya kamata.
Sannan ta sama wa matasa sama dubu 4 aikin yi a fadin Nijeria a dukkan matakai na kasa.
Duka wannan kokari da Ambasadar ke yi na gani ta tallafa wa masu karamin karfi, kudaden duk da take kashewa tana samunsu ne ta hanyar kasuwancinta da kuma sauran hanyoyi na neman halali.
Sannan an gabatar da wasu daga irin kayayyakin da ta raba da suka hada da kayan makarantar almajirai (Uniform) da take dinkawa na tsangaya musanman a yankunan karkara da sauransu, da kuma sauran sabbin tsare-tsaren ayyukan da za ta gabatar nan gaba.
A karshe Ambasada Goni da mika wa Mai Martaba Sarki Mukamin Uban Wannan Kungiya wato (Grand Patron).
Da take magana da wakilin LEADERSHIP Hausa ta ce wannan aikin ma somin tabi a nan Jigawa domin yanzu ma ta fara, za kuma ta ci gaba kamar yadda yi a fadin jihohin Nijeriya baki daya.
Daga ‘yan Majalissar Sarki da suka tarbe ta akwai Mai Girma Galadiman Dutse, Wamban Dutse, Madaki, Dan Kwano, Sa’i, Dan Masani, Barnawa, Sarkin Fada, Magatakarda, da kuma Jakadan Sulhu.