Rundunar ‘yansndan Jihar Kano ta gurfanar da mutum 104 da ake zargi ‘yan daba ne a gaban wasu kotuna da ke unguwar Nomandsland a Jihar.
An kama mutanen a wuraren hawan sallah da masarautun Kano ke yi duk shekara a bukukuwan sallah.
- Ƙungiya Ta Ƙaddamar Da Rabon Tallafi A Jigawa
- Yadda Bayern Munich Ta Hana Arsenal Rawar Gaban Hantsi A Gasar Zakarun Turai
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne, ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook, inda ya ce ana zargin mutanen da laifukan daba da rike makamai da kuma ta’amali da miyagun kwayoyi.
Kiyawa, ya ce an samu kama mutanen ne bayan binciken da aka yi a sashen binciken manyan laifuka na rundunar kamar yadda kwamishinan rundunar, CP Mohammed Usaini Gumel ya umarta.
A baya-bayan nan ma rundunar ta Kano ta kama wasu da ta ce ‘yan daba ne wadanda kuma suke addabar unguwar Dorayi.