A yau Alhamis, aka kammala bikin baje kolin kayyayakin amfani na kasa da kasa na Sin karo na 4, wanda ya shafe tsawon kwanaki 6.
A matsayinsa na katafaren baje kolin kasa da kasa na farko a kasar Sin a bana, kuma wani muhimmin bangare na “shekarar inganta sayyaya” , yawan kayayyakin da aka baje kolinsu da adadin sabbin kayyayaki da aka kaddamar da ma yawan masu ziyara duk sun kai wani sabon matsayi, wanda ya nuna dimbin karfin da kasuwar sayayya ta kasar Sin ke da shi.
Kamfanoni daga kasashe da dama na duniya sun halarci baje kolin na bana, kuma yawan kayayyakin da aka baje ya kai wani matsayin koli a tarihi. Fadin wurin baje kolin ya kai muraba’in mita dubu 128, inda fitattun kamfanoni 4019 daga kasashe da yankuna 71 suka hallara. A bana, adadin kasashen da suka hallarci bikin ya karu da kaso 9, inda na kamfanoni ya karu da kaso 19, idan aka kwatanta da baje kolin karo na 3. Haka kuma, an samu masu sayyaya da yawansu ya zarce dubu 55, karuwar kaso 10 idan aka kwatanta da karo na 3 na bikin. (Fa’iza Mustapha)